Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiFiye Da Mutum 11,000 Ne Masu Neman Aiki A Hukumar Yaki Da...

Fiye Da Mutum 11,000 Ne Masu Neman Aiki A Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Kano- Inji Muhyi Magaji

Daga Abdullahi Inuwa

Shugaban Hukumar Kula da Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci ta Jihar Kano, Barrister Muhyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa fiye da mutane 11,000 ne suka nemi aiki a matsayin 100 da hukumar ke shirin cike wa cikin kwanaki 3 kacal.

Hukumar ta bude dandalin neman aiki ne a ranar 7 ga Afrilu, kuma zai rufe a tsakar dare ranar Lahadi. Muhyi ya ce a ranar Alhamis da yamma, mutane 10,757 sun nemi aikin, kuma da karfe 10 na dare, adadin ya kai 11,000.

Rimin Gado ya danganta yawan masu nema da karuwar rashin aikin yi a cikin al’umma. Ya kara da cewa sun yanke shawarar bude dandalin neman aikin a kan layi domin tabbatar da adalci ga kowa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments