Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiMa’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista

Ma’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista

Rukkanin ministocin ma’aikatun jin-ƙan Najeriya, babu wanda ba a zarga ba da karkatar da kuɗin al’umma.

Tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Nduese Essien, ya ce Ma’aikatun Harkokin Jin-ƙai na tarayya da jihohi sun zamo matattarar cin hanci da rashawa a Nijeriya.

Essien, ya kuma zargi ministocin ma’aikatun da karkatar da biliyoyin naira da aka ware domin ‘yan ƙasar da ke cikin mawuyacin hali.

“Wani zai yi tunanin ƙirƙirar ma’aikatun nan zai inganta rayuwa da walwalar al’umma, amma abun takaici sun zamo mazurarar sace kuɗin al’umma ba tare da wata shakka ba.

“Dukkanin ministocin ma’aikatun jin-ƙan Najeriya, babu wanda ba a zarga ba da karkatar da kuɗin al’umma.” In ji shi.

Kazalika ya soki shirin ‘yan siyasa na raba jari ga talakawa, yana mai cewa suna yi ne don boye gazawar gwamnati na samar da abubuwan more rayuwa da damarmaki ga al’ummarsu.

Aminiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments