Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Zulum, Shehun Borno sun yi Allah wadai da sabbin hare-haren Boko...

Gwamna Zulum, Shehun Borno sun yi Allah wadai da sabbin hare-haren Boko Haram

Gwamnan jihar Borno Gwamna, Babagana Umara Zulum, da Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, sun bayyana mattukar damuwa game da sabbin hare-haren kungiyar Boko Haram da ISWAP a baya-bayan nan, inda suka bukaci gwamnatin tarayya da jami’an tsaro da su dauki mataki kafin lamarin ya kuskura.

A ‘yan watannin nan ‘yan tada kayar baya sun kai munanan hare-hare a kauyuka da sansanonin sojoji, musamman a garin Sabon Gari, Wajiroko da Wulgo da dai sauransu.

Yayin wani taron tsaro da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar Borno, Gwamna Zulum ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ba da fifiko kan harkokin tsaro a yankin Arewa maso Gabas, musamman jihar Borno, wanda take makwabtaka da kasashe uku da suka hada da Chadi, Kamaru da Jamhuriyar Nijar da kuma kalubalen tsaro a yankin Sahel.

“Duk da cewa muna godiya da irin dimbin tallafin da gwamnatin tarayya da sojoji suka bayar, muna kuma fatan bayyana cewa yanzu da aka karkata akalar yaki da ta’addanci daga yankin Arewa maso Gabas, duk matakan da aka dauka zuwa yanzu yana koma baya.”

“A ‘yan kwanakin nan jihar Borno ta sha fama da hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram, an kawar da dakaru da dama, kamar su Wulgo, Wajiroko da Sabon Gari, da dai sauran su. Ga dukkan alamu lamarin ya fara tabarbarewa.

“Saboda haka, muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta mayar da hankali kan yankin Arewa maso Gabashin kasar nan. Da alama rundunar sojojin Najeriya da ma’aikatar tsaro ba ta arewa maso gabas suka mayar da hankali ba.

Gwamna Zulum ya ce yankin Arewa maso Gabas, musamman jihar Borno mai makwabtaka da kasashe uku a yankin sahel ya cancanci gwamnatin tarayya ta kula da tattaunawar da ake yi na yaki da ta’addanci a Najeriya.

Zulum ya kara da cewa, “Harin da ‘yan Boko Haram ke ci gaba da yi a jihar abu ne mai matukar damuwa, ana bukatar daukar kwakkwaran mataki na soji domin yakar ‘yan ta’addan, hare-haren na baya-bayan nan sun addabi Sabongari, Damboa, Wulgo da Baga.

“Ina kira ga sojojin mu da su kasance ba kawai su kafa shingayen binciken ababen hawa da tsare garuruwanmu da kauyukanmu ba, ina kuma kira ga sojojin mu da su kai farmaki ga abokan gaba, kada mu ba wa ‘yan ta’addan numfashin domin su sake haduwa, su kwato makamai da kai hare-hare a yankunanmu. cikas,” Zulum yace.

Gwamnan ya jaddada kudirin sa na ci gaba da tallafawa sojoji da sauran jami’an tsaro da ke aiki a jihar Borno domin cimma burinsu na yaki da ta’addanci a jihar.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, “Gwamnatin jihar Borno za ta ci gaba da hada kai da sojojin kasar wajen aiwatar da shirye-shiryenmu na ci gaba da samar da zaman lafiya, muna sane da alakar ci gaba, tsaro da zaman lafiya, don haka muna saka hannun jari a muhimman ababen more rayuwa, muna kuma bude sabbin hanyoyin da ‘yan kasar za su iya shiga harkar noma da kuma dogaro da kai.

Ya kara da cewa, “Duk wadannan ba za su yiyu ba, ba tare da samar da kayan aiki da kuma baiwa jami’an tsaronmu damar tabbatar da tsaron yankinmu da kuma kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa ba, gwamnati ta za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro tare da tura su aiki mafi kyau a lokacin da suka fuskanci ta’addanci, tada kayar baya da kuma aikata laifuka.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron tsaro na sirri, kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida na jihar Borno, Farfesa Usman Tar, ya bayyana cewa daga cikin kudurori da aka cimma a karshen taron, majalisar ta bayyana goyon bayanta ga kokarin sake tsugunar da gwamnatin jihar Borno.

Taron ya samu halartar GOC 7 Div, Manjo Janar Abubakar Haruna, da sarakunan gargajiya daga masarautun Borno 7 da sauran shugabannin hukumomin tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments