Daga RABIU SANUSI
Sabon Hakimin Bichi da aka naɗa, Alhaji Munir Sanusi Bayero, ya karɓi ragamar mulki a hukumance, inda ya sake jaddada biyayyarsa ga Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, tare da yin alkawarin riƙe darajar daɗaɗɗun al’adun masarautar Kano.
A cikin jawabinsa da ya gabatar a Bichi, Wamban Kano ya yi bayani kan tarihin muhimmancin garin Bichi, wanda tun daɗewa yake a matsayin wani ginshiki mai ƙarfi na masarautar Kano.
Ya tunatar da yadda sarakunan baya, ciki har da Sarkin Kano Abdullahi Bayero da Khalifa Sir Muhammadu Sanusi, suka yi matuƙar daidaita alaka da Bichi, wanda hakan ya sa garin ya zama cibiyar gadon sarauta da shugabanci.
Alhaji Munir Sanusi Bayero ya bayyana godiyarsa ga Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, bisa amincewa da nauyin da aka ɗora masa.
Ya yaba wa Sarkin bisa cikakken goyon bayansa tun daga lokacin da aka naɗa shi a matsayin Dan Maje, har zuwa matsayinsa na Wambai. Ya kuma jaddada muhimmancin aminci da biyayya, yana tuna irin jarabawar da suka sha tare da Sarkin a lokacin baya da kuma farin cikin da suka yi bayan dawowarsu Kano.
“Gadon sarautarmu da asalin danginmu yana nan daram ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba. Haɗin kai da hadin gwiwa da ya shimfiɗa tsakanin ‘ya’yan sarki alama ce ta hikimarsa da basirarsa,” in ji shi.
Ya bukaci zuriyar masarautar da su ci gaba da kasancewa tsintsiya maɗaurinki ɗaya, tare da goyon bayan jagorancin Sarkin. Ya yi gargadin cewa a guji rarrabuwar kawuna da tasirin waje da ka iya haddasa rabuwar kai a cikin gidan sarauta.
A matsayin sa na Hakimin Bichi, ya yi alkawarin bin sahun magabatansa, musamman Yayansa, Wambai Abubakar, wajen ba da fifiko kan ilimi, samar da ayyukan yi, da shirye-shiryen jin daɗin al’umma. Ya jaddada kudirinsa na ci gaba da aiwatar da hangen nesa na Sarkin Kano, musamman a ɓangaren inganta ilimi da kiwon lafiyar yara.
Har ila yau, Wambai ya nuna godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa rawar da ya taka wajen dawo da darajar masarauta da kuma ci gaban ilimi a jihar. Ya yabawa gwamnan bisa jajircewarsa a shugabanci, tare da tabbatar da goyon bayansa ga shirye-shiryen ci gaban da gwamnatin jihar ke aiwatarwa a Bichi.