Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
A wani bangare na shirin ciyar da abinci ga masu kananan karfi a azumin watan Ramadan, ma’aikatar kula da harkokin addini da da’a ta jihar Yobe ta fara rabon kayan abinci ga cibiyoyi dari da biyu da aka ware a fadin jihar wanda ake ciyar da mutane dubu hamsin da daya a kullum abincin buda baki.
Kwamishinan ma’aikatar, Alhaji Yusuf Umar Potiskum ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai wadda babban sakataren dindindin na Ma’aikatar Alhaji Yusuf Hassan Yusuf ya wakilta, ya ce ciyar da buda baki na daga cikin kokarin tallafawa marasa galihu a cikin watan Ramadan.
Ya ce gwamnati ta amince da ware naira miliyan dari biyu da casa’in da bakwai 297,000,000,00 don shirin ciyar da azumin watan Ramadan na shekarar 2025 a fadin kananan hukumomi goma sha bakwai na jihar.
Kwamishinan ya bukaci kwamitin da ya hada kai da shugabannin gargajiya da na addini a cibiyoyinsu daban-daban domin yin amfani da kayan abinci yadda ya kamata da nufin ciyar da mutane dari biyar a kowace cibiya.
A cewarsa gwamnati ta kuma samar da kudi domin jigilar kayan abinci zuwa cibiyoyin da aka kebe.
Kwamishinan ya kuma kara da cewa a bana an kara wuraren buda baki zuwa dari da biyu a kan cibiyoyi tamanin da shida da suka gabata, inda ya nuna cewa baya ga kayan abinci an ware naira dubu talatin ga kowace cibiyar ciyarwa a kullum.
Ya yabawa gwamna Mai Mala Buni bisa baiwa ma’aikatar dukkan goyon bayan da suka dace don sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.