Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna
Fitaccen ɗan jarida kuma ɗan siyasa, Malam Yusuf Abubakar Dingyaɗi ya koka da yadda Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) take yi wa Musulmi kutse a kan ‘yancinsu.
Ya ce hakan ya faru ne sanadiyar rashin haɗin kai na Musulmin Najeriya da yadda rarrabuwar kawunan Malamai take ƙara ta’azzara, suna cin zarafin junansu.
A wata takardar ƙorafi da ya aikawa manema labarai , Dingyaɗi, wanda shi ne Magayaƙin Garkuwan Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya ce “Baki ɗaya yanzu ana ci gaba da wulaƙanta rinjayen Musulmi saboda ba mu da murya ɗaya mai ƙarfi.”
Ya ci gaba da cewa, “An yi amfani da siyasa don wargaza mana mutunci. Sai kuma son rai a shugabanni da ke amfani da ikonsu wajen cin zarafin wasu daga cikin shugabannin da suke da girma a fuskar al’umma.”
Malam Yusuf ya buƙaci al’ummar Musulmi da su haɗa kai domin kare mutunci da martabar kansu. Kamar yadda ya nemi ƙungiyar ta CAN da ta tsaya a matsayinta, ta daina shisshigi ga lamarin da ya shafi al’ummar Musulmi, domin a zauna lafiya da mutunta juna.