Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Shugaban hukumar koyarwa ta Jihar Yobe Alh. Yakubu Dokshi ya ce an karawa malaman makaranta kimanin 1,000 Karin girma zuwa matakai daban-dabam. “Ina mai farin cikin sanar da ku cewa an kara wa malaman makaranta 1000 girma a makarantunmu daban-dabam da ke jihar,” inji shi.
Shugaban hukumar ya bayyana haka ne a lokacin wani taron gudanarwa na hukumar a Damaturu.
Alhaji Yakubu Dokshi ya ce karin girma ga ma’aikatan koyarwa na daga cikin kokarin gwamnatin Buni domin bunkasa kwazon ma’aikatan da zimmar inganta aikin koyarwa.
Ya kuma jaddada cewa mahukuntan hukumar sun jajirce wajen ganin an baiwa malamai tallafin da ake bukata tare da kwadaitar da su wajen aiwatar da aikin da aka ba su yadda ya kamata.
Dokshi ya yabawa gwamna Mai Mala Buni da kwamishinan ilimi a matakin farko da na sakandire bisa jajircewarsu wajen bunkasa ilimi a jihar