Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Buni Ya Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwan Sha Na Buni...

Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwan Sha Na Buni Gari 

Daga, Sani Gazas  Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe  Mai Mala Buni a ranar Litinin din da ta gabata ne ya kaddamar da aikin samar da ruwan sha na Buni Gari, tare da kaddamar da aikin samar da aikin dakile ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a Buni Yadi da Damaturu fadar Jihar.

Madatsar ruwa ta Buni Gari na da karfin lita miliyan 243 tare da injin jawo ruwa kimanin lita 300,000 a kullum da za’a iya amfani da injinan janareta da Kuma tsarin amfani da hasken rana” .

Gwamna Buni ya ce an gudanar da aikin ruwan ne domin magance matsalar karancin ruwa da aka dade ana fama da shi a garuruwan Buni Gari, Buni Yadi da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da su.

“Na ji dadin yadda gwamnatinmu ta cika alkawarin da ta dauka a yakin neman zabe na gina madatsar ruwa ta Buni Gari da matatar ruwa domin kawo tallafi ga al’umma,” inji shi.

Gwamnan ya umarci al’ummomin da suka amfana da wannan aikin ruwa da su su kiyaye tare da kare aikin don amfanin ku da na baya”.

Da yake kaddamar da aikin samar da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a Buni Yadi da Damaturu, gwamnan ya ce “aikin zai magance matsalar ambaliyar ruwa da zaizayar kasa da kuma dakatar da barna a muhalli da kuma illolin da ke haifar da matsaloli a gonakai wajen  noma a tsakanin al’umma.

“A cika alkawuran da muka yi wa jama’a a lokacin yakin neman zabe cewa gwamnati za ta samar da dauwamammiyar mafita kan matsalar ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a wannan al’umma, gwamnatin jihar na zuba kudadenta wajen gina wannan aikin ba wai kawai don rage ambaliyar ruwa da zaizayar kasa ba, a’a har ma kuma da kokarin inganta ruwan da aka samu daga ambaliya domin bunkasa noman rani don samar da wadataccen abinci da wadatar tattalin arziki.

“Don haka an umurtan  ku da ku kula da wannan aikin, ku ba da hadin kai ga ’yan kwangila da kuma kare shi don samun fa’ida mafi yawa don tabbatar da zuba hannun jarin gwamnati a cikin aikin,” in ji Buni.

Buni ya kuma bayar da diyyar ga mutanen da aka karbi filayensu don gina wannan aiki Mai muhimmanci ga al’umma.

“Ina so in yaba musamman irin juriyar da al’ummomin da ambaliyar ruwan ta shafa saboda illar ambaliyar ruwa da zaizayar kasa da suka fuskanta.,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma kaddamar da rabon kayan amfanin gona da suka hada da takin NPK buhu 500, katan 85 na takin ruwa, famfunan ban ruwa mai amfani da hasken rana 115, injinan feshi guda1,000, iri iri iri na amfanin gona da kayan lambu 15, maganin ciyawa da magungunan kashe kwari ga manoman ban ruwa.

“Hakan ya kara nuna kudirin wannan gwamnati na ganin harkar noma ta Inganta don samun riba ga manoman mu,” inji Buni.

Haka nan Gwamnan ya kuma kaddamar da dakin gwaje-gwajen samar da ingancin ruwa a ma’aikatar albarkatun ruwa da ke Damaturu.

“A cewar sa gwamnatin ta samar da shi ne don tabbatar da ingancin ruwan da ake bayarwa ga jama’a don kyautatuwar lafiyar su wadda dakin gwaje-gwajen za a yi bincike ne kan cututtukan da ke tattare da ruwa, wanda hakan ya sa jihar ta cika dokokin ruwa da tsaftar muhalli na duniya.”

Ina so in yi amfani da wannan dama wajen sake tabbatar muku da cewa, gwamnati za ta ci gaba da samar da tsaftataccen ruwan sha a fadin jihar domin inganta lafiyar al’ummarmu.” in ji Buni.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments