Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeTsaroAU Zata Tallafawa Dakarun MNJTF Dan Yakar Ta'addanci A Tafkin Chadi

AU Zata Tallafawa Dakarun MNJTF Dan Yakar Ta’addanci A Tafkin Chadi

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi alkawarin bayar da tallafin dala 800,000 ga rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF), domin karfafa yakin yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi.

Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afirka, Amb.  Adeoye Bankole ne ya bayyana haka a wajen bude taron gwamnonin tafkin Chadi karo na 5, a Maiduguri, fadar Jihar Borno.

Ya kuma tabbatar da ci gaba da bayar da tallafin kudi da kayan aiki na kungiyar ta AU ga dakarun MNJTF, inda ya kara da cewa irin wannan tallafin ya taka muhimmiyar rawa wajen yakar Boko Haram da sauran barazanar ta’addanci.

Kwamishinan ya jaddada cewa tun a shekarar 2015, MNJTF ta taka rawar gani wajen tabbatar da tsaro a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula, da dakile munanan hare-hare, da kuma samar da hanyoyin samar da zaman lafiya.

Ya ce hukumar ta bayar da tallafi mai dorewa ga rundunar tun lokacin da aka kafa ta, inda ya ce za ta kara ba da karin dala 800,000 domin kara karfafa ayyukan ta.

Ya kara da cewa, tallafin, zai karawa Kungiyar MNJTF karfin gwiwar  gudanar da ayyukan ta na yaki da ta’addanci, inganta musayar bayanan sirri, da tallafawa kokarin tabbatar da yankin.

Ya jaddada bukatar gwamnatocin yankin tafkin Chadi da su hada kai don dakile ayyukan ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya a cikin kasafin kudin kasarsu, domin tabbatar da tsaro da tsayin daka kan harkokin dawo da zaman lafiyar yankin na tafkin

A jawabin sa babban sakataren hukumar tafkin Chadi LCBC Ambasada Mamman Nuhu ya yaba da rawar da kungiyar gwamnonin tafkin Chadi ke takawa wajen samar da tattaunawa, hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da samun nasarar aiwatar da dabarun tabbatar da zaman lafiya a yankin (RSS), taswirar hanya da aka tsara don magance tushen rashin zaman lafiya a yankin.

Ya zayyana muhimman nasarori da suka hada da tsare-tsare na farfado da rayuwa, samar da zaman lafiya da mutunci na mutanen da suka rasa matsugunansu da inganta tsaro.

Sai dai ya yi gargadin cewa har yanzu akwai gagarumin kalubale musamman yadda Boko Haram suka sake kunno kai a wasu yankunan, inda ya kara da cewa, “wannan dandalin ba wai kawai dandalin tattaunawa ba ne, shi ne zai kawo dauki.

“Sakamakon Boko Haram ya nuna cewa rashin zaman lafiya a wani yanki na yankinmu ya shafi tudun mun tsira saboda haka tilas ne mu mayar da martanin mu wajen hada Kai a yankin na tafkin Chadi.”

Ya jaddada bukatar yin hadin gwiwa a kan iyakokin kasashen biyu wajen tunkarar barazanar tsaro, sarrafa albarkatun kasa, da rage hadurran da suka shafi yanayi.

Don haka ya bukaci kasashe mambobin kungiyar da su kara zuba jari a shirye-shiryen tabbatar da zaman lafiya tare da tabbatar da an karkatar da albarkatu a inda ake bukatar su.

“Abin bukata ga gwamnatoci shine tsaiwar daka haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki da yawa ciki har da ƙungiyoyin jama’a, kamfanoni masu zaman kansu, da abokan aikin jin kai da ci gaba don samar da kwanciyar hankali na dogon lokaci.”

Ya kuma yabawa kungiyoyi da abokan huldar kasa da kasa kan goyon bayan da suke ci gaba da bayarwa, yana mai jaddada cewa, matakin ya taimaka matuka wajen rage wahalhalu, da maido da zaman lafiya mai dorewar a yankin.

Ambasada Mamman Nuhu ya ba da shawarar bin  ingantattun hanyoyin sa ido da tantancewa don tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin aiwatar da shirye-shiryen dawo da zaman lafiya da ake yi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments