Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaNa Fasa Fita Jam'iyyar APC Sakamakon Sa Bakin Gwamna Buni--- Inji Hon...

Na Fasa Fita Jam’iyyar APC Sakamakon Sa Bakin Gwamna Buni— Inji Hon Jakusko

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Tsohon Darakta Janar na kungiyar gangamin wayar da kan jama’a na Jam’iyyar APC a Jihar Yobe kuma shugaban jam’iyar APC a mazabar Jaba/ Muguram a karamar hukumar Jakusko Hon. Saidu Hassan Jakusko, ya janye batun murabus dinsa daga jam’iyyar bayan da ya mika takardar yin hakan a ranar Jumu’a kasa da mako guda da ya sanar da ficewar sa daga Jam’iyyar ta APC.

A cikin wannan wasika da ya fitar a ranar Juma’a, Hon. Jakusko ya bayyana janye kudirinsa na murabus din da ya yi daga cikin Jam’iyyar APC sakamakon koken da ya yi na rashin martaba shi, shi da wasu magoya bayan sa da jam’iyyar ta APC ba ta yi.

“Ina matukar godiya ga mai girma Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe da dangane da irin kokarin sa na ganin Jam’iyyar APC ta ci gaba da dunkulewa wuri guda ba tare da samun kowace irin farraka ba, kana ina kuma kara godiya ga mataimakin gwamnan Jihar Yobe, Hon.  Idi Barde Gubana, saboda irin rawar da ya taka wajen ba ni damar saurare da kuma jagorancin da in sauya shawarar da na yi tun  farko na barin Jam’iyyar,” in ji Hon Jakusko .

Ya kuma mika godiyarsa ga tsohon dan majalisar wakilai Hon.  Zakari Ya’u Galadima, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin matasa, Hon.  Hashimu Nuhu Hashimu, da sauran mutanen da suka shiga cikin lamarin.

“Ina so in ba da hakuri ga duk wanda ya ji haushin abin da na yi a baya,” in ji Jakusko.

A tattaunawar sa da Aminiya Jim kadan da jinye wannan kudiri na sa na ficewa daga jam’iyyar ta APC Sa’idu Hassan ya ce, dalilinsa na barin Jam’iyyar a baya shine rashin  kula da bukatun al’ummar sa ne da kuma shi kan sa duk da dimbin gudummawar da ya ke bayarwa ga nasarar Jam’iyyar a dukkannin zabukan da aka gudanar a baya tun daga 2019 zuwa ga yau.

“To amma da ya ke gwamna Mai Mala Buni shugaba ne da ya san muhimmancin mutane da jim labarin wannan lamari nawa nan da nan ya sa baki wajen kokarin ganin ya magance wannan matsala tare da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar wadda hakan ne ya sa na yanke shawara ajiye makamai na ta wajen janye wannan kudiri nawa na ficewa daga Jam’iyyar ta APC.”

Don haka ya bada tabbacin cigaba da bada goyon bayan sa tare da bada gudummawar sa ga Jam’iyyar ta APC don ganin ta cigaba da daure banten ta na samun nasara a dukkan zabukan ta in Allah ya so.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments