Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Buni Ya Jajantawa Iyalan Wadanda 'Yan Fashi Suka Kashe 'Yan Uwan...

Gwamna Buni Ya Jajantawa Iyalan Wadanda ‘Yan Fashi Suka Kashe ‘Yan Uwan Su A Kasuwar Ngalda

Daga, Sani Gazsa Chinade, Damaturu

Akalla mutane bakwai ne suka mutu sannan goma sha daya suka jikkata a wani hari da ‘yan fashi da makami suka kai a kasuwar Ngalda da ke karamar hukumar Fika a jihar Yobe.

Wadannan ‘yan fashi da makamin dai sun kai harin ne don sace dukiyoyin mutane a yammacin ranar litinin a daidai lokacin da kasuwar ke shirin tashi.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun bude wuta kan ‘yan kasuwa da masu shaguna, lamarin da ya haifar da firgici da hargitsi.

A halin da ake ciki gwamna Buni ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu tare da jajantawa wadanda suka jikkata.

Ya kuma umurci gwamnatin jihar da ta bayar da tallafi ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Gwamnan ya kuma umarci hukumomin tsaro da su binciki musabbabin lamarin tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya don girbar abin da suka shuka.

“Ya kamata ku yi cikakken bincike, ku binciki irin hanyoyin da za a bi don kiyaye afkuwar irin ya hakan nan gaba, ” inji Gwamna Buni.

Kasuwar Ngalda ita ce babbar kasuwar dabbobi a yankin, inda ake samun ‘yan kasuwa daga jihohin da ke makwabtaka da su na zuwa domin saye da sayarwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments