Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLafiyaTawagar Likitocin Gidauniyar Madakin Gudi Sun Ceto Rayuwar Wani Almajiri A Jihar

Tawagar Likitocin Gidauniyar Madakin Gudi Sun Ceto Rayuwar Wani Almajiri A Jihar

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Tawagar jami’an gidauniyar Madakin Gudi, karkashin jagorancin Malam Hassan Kaku, ta sake ziyartar babban asibitin Gashua domin duba lafiyar wani yaro Almajiri bayan an yi masa tiyata.

A yayin ziyarar, ƙungiyar ta tabbatar da cewa lafiyar majiyyaci tana inganta sosai.

Wani dan uwa ga Hamza Sadik  Malam Sadiq Mohammed, wanda ke tare da shi a asibitin ya yaba da kokarin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni da Gidauniyar Madakin Gudi bisa wannan shiri na Ceto rayuwar Dan uwansa.

Malam Sadiq Mohammed ya kara da cewa, idan ba don tsoma bakin da gwamnatin jihar Yobe da gidauniyar Madakin Gudi suka yiwa Hamza ba, da watakila lafiyarsa ta shiga wani hali mai tsanani a halin yanzu.

Idan dai za a iya tunawa wasu gungun kwararrun likitoci ne suka ceci ran wannan yaron Almajiri da aka yi watsi da shi mai suna Hamza Sadik  a lokacin da suka  je ziyarar aiki a karamar hukumar Yusufari a jihar Yobe.

Hamza, dalibi ne  Almajiri dan shekara goma sha hudu a Tsangayar Malam Ilu da ke garin Yunusari, yana cikin mawuyacin hali sakamakon wata jinya da ya ke fama da ita da ke da alaka da cutar zazzabin taifod (Typhoid) tsawon lokaci ba tare da an kula da shi ba.

Cutar dai ta kusa kashe yaron ne a lokacin da wani mutumin kirki mai suna Malam Nuhu Musa ya kai shi babban asibitin Yusufari don duba lafiyar sa.

An yi sa’a, an kawo Hamza asibitin ne a ranar da tawagar likitocin da gidauniyar Madakin Gudi Foundation ta shirya ke gudanar da aikin ba da jinya kyauta a garin Yusufari wanda wani bangare ne na aikin jinya kyauta a fadin jihar.

Nan da nan bayan ganin Hamza cikin wannan mawuyacin hali sai  babban Likitan gidauniyar MK Abdullahi ya duba lafiyarsa, sannan ya gano matsalar daga bisani likitan ya mika yaron zuwa asibitin kwararru da ke Gashuwa.

Majiyar na cewa, lokacin da aka Kai Hamza asibiti bayan da aka gano irin jinyar da ya ke fama da ita Nan da nan aka yi masa tiyata wanda ya samu nasara kuma yana samun sauki ya zuwa yanzu.

 

 

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments