Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamnatin Borno Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 9.6 Don Bayar Da...

Gwamnatin Borno Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 9.6 Don Bayar Da Tallafin Karatu A 2024-wakilbe

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum ta kashe kimanin Naira biliyan 9.7 wajen bayar da tallafin karatu ga daliban ‘yan asalin jihar da ke karatu dabam-dabam a manyan makarantun karo Ilimi a kasar nan da wajen kasar nan a shekarar 2024.

Kwamishinan Ilimi, kimiyya, fasaha da kere-kere, injiniya.  Lawan Abba Wakilbe ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa na 2025 na farko da Gwamna Zulum ya jagoranta a gidan gwamnati dake Maiduguri babban birnin jihar.

A cewar sa jimillar dalibai 30,616 da suka yi karatun digiri na farko a Jami’o’i, Kwalejojin Ilimi da na kimiyya da sauran cibiyoyi na karo karatu a cikin Najeriya, wadanda ke karatun shari’a, kimiyya, likitanci, jinya (Nursing), da Injiniya sun sami naira biliyan 4,289,243,200 a matsayin tallafin karatu.

Bugu da kari, dalibai 335 na cikin gida da suka kammala karatun digiri na biyu a fannin kimiyya, fasaha, Injiniya, da lissafi (STEM) an ba su tallafin naira miliyan 382.

Dangane da tallafin karatu na kasa da kasa, an raba naira biliyan 2,325,467,300 ga dalibai 132 da ke karatun digiri na farko a fannin likitanci da injiniya a jami’o’i a kasashen Sin da Masar.

Bugu da kari, dalibai 287 da suma suka yi rajista a kwasa-kwasan da ke da alaka da kimiyya da fasahar a Indiya da Malaysia sun samu naira biliyan 2,691,467,300.

Haka nan dalibai 31,369 ne suka ci gajiyar shirin bayar da tallafin karatu a shekarar 2024, inda tuni gwamna Zulum ya amince da daukar nauyin sabbin dalibai sama da 30 wadanda za su ci gaba da karatu a fannin sufurin jiragen sama a shekarar 2025.

Da yake karin haske kan wasu cibiyoyi da ke karbar bakuncin wadanda suka amfana, injiniya Wakilbe ya bayyana cewa a halin yanzu dalibai 997 ne ke karatu a kwalejin koyon aikin jinya da ke Maiduguri, tare da wasu 94 a asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH).

Hakazalika daliban likitanci 32 ne ke halartar Jami’ar Al-Ansar da ke Maiduguri, yayin da dalibai 392 ke karatu a kwalejin kimiyya da fasaha  ta gwamnatin tarayya (Federal Polytechnic) Monguno.

Dangane da tallafin karatu na kasashen waje, “kimanin dalibai 150 suna karatu a Indiya, tare da 19 suna  suna karatun aikin likitanci, 29 a Malaysia, 65 a Jami’ar Sharda, da 85 a Jami’ar Integral a kasar Indiya.

Haka nan a kasar Sin  (China), dalibai 10 sun shiga cikin shirin MBBS a Jinzhou  Jami’ar kiwon lafiya, 30 a Jami’ar Anhui, da ɗalibai 50 suna karatun Injiniya a Jami’ar Naijing da kuma a Jami’ar fasaha ta Liaoning, da jami’ar fasaha ta Hefei”, in ji Hon.  Wakilbe.

Kwamishinan ya jadadda cewa wadannan guraben karo karatu da ke tare da su za su taimaka wajen biyan bukatun ma’aikata a jihar, musamman yadda Jihar ta farfado daga kalubalen ‘yan tada kayar baya.

Shirin ya yi daidai da ajandar kawo sauyi na shekaru 10 da kuma shirin raya kasa na shekaru 25 da gwamna Zulum ya kudirta, domin tabbatar da kyakkyawar makoma ga jihar Borno da al’ummarta.

Kwamishinan ya ce, baya ga wannan karimcin, an gina makarantu na zamani dake dauke da ajujuwa, tare da daukar kwararrun malamai a kananan hukumomi da yawa da ke Jihar a fadin mazabun majalisar dattawa  uku da ke jihar tare da rage yawan yara wadanda ba sa zuwa makaranta daga kan titunan Jihar.

Ya yabawa gwamna Zulum da duk masu ruwa da tsaki ciki har da sakataren zartarwa na hukumar bayar da tallafin karatu ta Jihar Borno, Malam Bala Isa bisa samar da damammaki ga dalibai da iyaye wajen samun nutsuwa yayin da suke ci gaba da karatunsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments