Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarim Lawan, ya sha alwashin ci gaba da yin kira ga gwamnatin tarayya da ta kwato yankin karamar hukumarsa ta Guzamala daga hannun ‘yan Boko Haram.
Kamar yadda wani rahoto ke nunawa karamar hukumar Guzamala da shugaban majalisar ya fito ta fi Abuja babban birnin tarayyar Najeriya girma fiye da sau uku a fannin filaye kuma ta shafe sama da shekaru 10 tana karkashin mamayar mayakan Boko Haram.
Domin ceto lamarin, Lawan yana kira da a gaggauta kafa rundunar soji a yankin karamar hukumarsa, wannan matakin a cewar Lawan na da nufin yin amfani da dimbin sojojin da suke da su wajen yakar kungiyar ta ‘yan ta’adda da karfin Allah da kuma karfin dakarun sojan Najeriya.
Kakakin majalisar ya sake yin kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Maiduguri.
A cewar sa, “Ina kira ga gwamnatin tarayya da sojojin Najeriya da su gaggauta kafa barikin soja na musamman a Guzamala, domin ta haka ne kawai za a iya gaggauta dawo da ‘yan gudun hijirar zuwa gidajen kakanninsu.
“A halin yanzu, babu wani nau’i na tsaro a Guzamala ko kadan, al’ummar mazabata suna zaune a sansanonin ‘yan gudin hijirar (IDPs) da al’ummomin da suka karbi bakuncin fiye da shekaru 10 yanzu.
“Don haka Ina rokon gwamnatin tarayya ta yi gaggawar ’yantar da mazabata,” in ji Lawan.
Shugaban majalisar ya bayyana cewa a karshen shekarar da ta gabata mayakan Boko Haram sun kai hari tare da korar mazauna garin Mairari- daya daga cikin kauyukan da ke karkashin Guzamala, inda gwamna Babagana Zulum ya mayar da wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar zuwa gidajen su.
Ya yaba wa gwamna Zulum bisa kokarin da ya yi na dawo da wasu ‘yan gudun hijirar yankunan Guzamala amma ya ce gwamnan “ba shi da iko da sojoji don haka yana da iyaka a kokarinsa na mayar da jama’ata ya zuwa gidajen kakanninsu.”
Shugaban majalisar ya kuma bayyana dalilan da suka sa majalisar dokokin jihar ta yi jinkirin sakin kudirin kasafin kudin jihar na farko na 2025 sai da ta yi karin sama da Naira biliyan 30 inda ya ce akwai bukatar a kara kason kasafin kudin ga wasu muhimman sassa.
Ya bayyana cewa karin ya biyo bayan wani kwakkwaran nazari da kwamitin kasafin kudi na majalisar ya yi tare da hadin gwiwar sauran kwamitoci.
Ya zama dole a ware karin kudade ga muhimman wurare da aka yi watsi da su a cikin kudurin kasafin kudin na farko,” in ji Lawan.
“Ma’aikatar lafiya ta samu karin Naira biliyan 7 domin inganta harkokin kiwon lafiya a jihar, musamman don samar da kayan aiki da sabon asibitin koyarwa na jihar Borno da kuma gudanar da sabbin cibiyoyin kiwon lafiya da aka gina a fadin kananan hukumomin Jihar.
“Bayan Naira biliyan 5 ga ma’aikatar yaki da fatara da ci gaban matasa ya zama abu mafi muhimmanci idan aka yi la’akari da kalubalen tattalin arziki, inda ya jaddada cewa kudaden na da matukar muhimmanci wajen magance talauci da ya ta’azzara saboda rashin tsaro na tsawon shekaru a jihar.
“Jihar Borno ta fuskanci matsanancin talauci saboda rashin tsaro, yadda karin rabon zai tallafa wa shirye-shiryen da ke da nufin samar da rayuwa mai dorewa da karfafawa ‘yan kasa, musamman matasa,” inji shi.
“Asusun amintattu na tsaro, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar rashin tsaro a jihar, ya samu karin naira biliyan 5 don inganta ayyukansa yayin da ofishin sakataren gwamnatin Jihar (SSG) da harkokin gwamnati su ma sun samu kaso mai tsoka.
“Haka nan asusun harkokin tsaro na tallafawa dabaru ga rundunar hadin gwiwa ta farar hula (CJTF), ‘yan banga, da sauran hukumomin tsaro yadda kudaden za su karfafa kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hanyar samar da ababen hawa, man fetur, da sauran bukatu na aiki,” in ji shugaban majalisar.