Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Mai martaba sarkin Fika kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Jihar Yobe, Dokta Muhammad Ibn Abali Muhammad Idrisa, ya nada Alhaji Ali Adamu Fika a matsayin sabon wazirin masarautar Fika a Jihar Yobe
Shi dai sabon wazirin na Fika Alhaji Ali Adamu Fika, babban da ne ga marigayi Wazirin Fika, Malam Adamu Wazirin Fika, wanda shi ne tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya,
An haifi Ali Adamu Fika a ranar 2 ga Disamba, 1962, a Kaduna, ya yi karatun firamare a makarantar Kaduna Capital, ya yi sakandare a Barewa College Zariya, sannan ya yi digiri na biyu daga Jami’ar Maiduguri daga nan kuma ya yi PGDA da MBA a Jami’ar Ahmadu Bello.
Ali Adamu Fika ya yi ritaya daga aikin gwamnati a shekarar 2022, wanda ya shafe shekaru 33 yana aiki da sassan gudanarwa na hukumar Inshorar (NDIC) a shekarar 2022.
Tun daga nan ya sadaukar da lokacinsa wajen tallafa wa masarautar ta Fika da kuma al’ummar sa.
Nadin dai ya samu amincewa daga jama’a, inda jama’a suka yi dafifi zuwa gidan Ali Adamu Fika a Potiskum domin taya shi murna wadda ana kallon matakin da mai martaba sarkin ya dauka a matsayin wata shaida da ke nuna yarda da jagorancin Ali Adamu Fika da kuma jajircewarsa wajen ci gaban masarautar tsawon lokaci.


