Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Kungiyar kiristocin arewacin Najeriya reshen jihar Yobe ta samu tallafin buhunan shinkafa 1000 daga uwargidan shugaban kasa Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu.
Uwargidan shugaban kasar ta yi haka ne don tallafawa membobin kungiyar kiristoci don bikin kirsimeti.
Dokta Yahaya Galo, daya daga cikin mahalarta taron, ya shaida wa manema labarai a Cocin COCIN da ke Potiskum cewa za a raba shinkafar ga Kiristoci ba tare da la’akari da darikun su ba.
“Muna godiya ga sanata Tinubu da irin wannan karimcin kuma muna addu’ar Allah Ta’ala ya taimaka musu har tsawon zamansu a ofis,” inji shi.
Dr Yahya ya yi kira ga sauran masu rike da madafun iko su ma su rika kyuatatawa al’ummomin su musamman a lokuta irin haka don sa musu farin ciki a zukatan su.
Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, wanda ya yi magana a madadin fastoci da masu wa’azin bishara da suka yi ritaya a jihar, Usaku Yaro Kaku, ya yaba wa Sanata Oluremi Tinubu bisa wannan gudummawar da ta sanya a fuskar Kiristocin jihar Yobe.