Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayar da tallafin sufuri kyauta ga wasu da ba ‘yan asalin jihar ba su kimanin 710 , don ba su damar tafiya garuruwna su don bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara tare da ‘yan uwansu.
Shirin sufuri na kyauta wanda aka kaddamar a ranar asabar a tashar Bus Bus na Borno Express har kusan mutane kusan 285 ne aka fara da su zuwa sassa daban-daban na kasar nan, wanda kashi na biyu na mutan 285 za su yi tafiya a ranar lahadi, yayin da sauran za su tashi daga garin na Maiduguri a ranar litinin.
Da yake jawabi a lokacin kaddamar da shirin, shugaban kungiyar Ohaneze All Progressives Congress (APC) mai goyon bayan kungiyar, Cif Ugochukwu Egwidike, ya ce kowane daga cikin matafiya 710 baya ga shirin sufuri na kyauta zai karbi kudi N50,000, yayin da kusan mata 250 da mazajensu suka rasu da ba za su samu damar tafiya ba su ma kowaccen su an tanadar mata Naira 50,000 domin bikin Kirsimeti.
Egwudike ya kara da cewa gwamna Zulum ya samu gagarumin ci gaba wajen samar da tallafi ga mabukata da tsare-tsare daban-daban da nufin rage radadin talauci da inganta walwalar jama’a, kamar yadda ya ba da wannan tallafi ga harkokin sufuri a cikin karamar hukumar birnin Maiduguri, da kuma daukar nauyin dimbin Kiristoci zuwa Kudus domin gudanar da aikin ibada.
”Haka nan baya ga inganta harkokin sufuri a cikin birni, gwamnatin Gwamna Zulum tana bayar da tsarin sufuri kyauta ga duk wanda ba ‘yan asalin jihar ba a duk lokacin biikin kirsimeti irin wannan don haɗa kowane yanki na shiyyoyin shida na kasar nan a duk shekara.”
“Ya bayar da agajin gaggawa da albarkatu ga wadanda ba ‘yan asalin Jihar ba da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a jihar ba wadda wanna irin halayya na gwamna babban abin a yaba ne.”
Ya kara da cewa abubuwan da gwamnan ke nunawa sun nuna karara irin kokarin sa wajen gudanar adalci ga al’umma ga mazauna yankin ba tare da la’akari da kabila, addini da jam’iyya ba.
Shi ma Sarkin Yarbawa a jihar Borno, Alhaji Hassan Alao Yusuf shi ma ya yabawa gwamna Zulum bisa wannan karimcin, inda ya ce tsarin safarar mutanen da ba ‘yan asalin jihar ba ya nuna irin ayyukan alkhairai da Gwamnan ke aiwatarwa ga al’ummar Jihar da ma na sauran Jihohi.
Hakazalika, mamba a kwamitin amintattu na kungiyar jin dadin Igbo/Ohanaeze Ndigbo, jihar Borno, Pharm Napoleon Egbonu, ya yabawa Gwamna Zulum bisa yadda yake ci gaba da tallafa wa wadanda ba ‘yan asalin jihar ba.
Pharm Egbonu ya yi nuni da cewa irin wannan karimcin da gwamna ya yi wa wadanda ba ‘yan asalin jihar ba abu ne da ya kamata a yi koyi da shi da sauran gwamnoni wajen samar da amana da hadin kai a tsakanin kungiyoyin a fadin kasar nan.
Shima da yake nasa jawabin, Babban Manaja na Kamfanin Sufuri na Borno Express Grema Zanna, ya yabawa Gwamna Zulum bisa wannan karimcin, inda ya ce abin da gwamnan ya yi na daga cikin shirinsa na saukaka matsalar sufuri da tsadar kayayyaki ga mazauna jihar.
Ya yi nuni da cewa wadanda ke cin gajiyar shirin sufurin kyauta duk da kasancewar su ba ‘yan asalin jihar ba suna bayar da gudunmawar ci gaban tattalin arzikin jihar, kuma suna cikin jihar Borno wadanda ake zaman lafiya da su.