Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ce shekara ta 2025 da ke tafe gwamnati za ta dauki nauyin kammala dukkan ayyukan da ake gudanarwa da kuma sabbin ayyuka a kan kari domin cika alkawuran da ya yi wa al’ummar jihar a lokacin yakin neman zabe.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar litinin a yayin da yake rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2025 yadda ya zama doka, yana mai cewa, “wannan gwamnatin ta himmatu wajen yin amfani da gaskiya tare da saka hannun jarin albarkatunmu a cikin shirye-shirye da ayyuka na mutane, musamman, ilimi, samar da lafiya, noma, gudanar da abubuwan more rayuwa, samar da arziki. da ba da dama don tada ci gaban tattalin arziki.”
“Mun zayyana tare da tsara taswirar wasu albarkatu na noma da kiwo da sauran abubuwan da zai sa masu zuba jari a kasashen duniya za’a ba su damar samar da guraben ayyukan yi da samar da arziki yadda muka fara tattaunawa da manyan kungiyoyi na cikin gida da na kasa da kasa don amfani da wadannan abubuwan.”
“Bari na yi amfani da wannan dama domin jawo hankalin dukkan injiniyoyi masu sa ido da ke da alaka da ayyukan gwamnati, wadda makasudin ku kan wadannan ayyuka shi ne don kare muradun gwamnati, ku tabbatar da cewa an aiwatar da kowane aiki bisa ka’ida da sauran yarjejeniyoyin kwangila da aka cimma yarjeheniya akai yadda hakan zai tallafa muku don aiwatar da ayyukanku yadda ya kamata da inganci.
“Duk da haka, idan kun gaza a cikin ayyukanku, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sake samo injiniyoyi masu sa ido na waje don tabbatar da an aiwatar da ayyukanmu masu inganci don gwamnati ta cimma bukatun ta na gudanar da ayyuka ma su inganci da su yi dai-dai da kudaden da ta ware don hakan.”
“Ana kira ga kwamitin da ke sa ido kan ayyukan a karkashin jagorancin Engr. Zaji Bunu da su kara sanya ido a kan dukkan ayyukan ta yadda za a gudanar da ayyukan a kan ka’ida da kuma bin yarjejeniyar kwangilar da aka kulla domin karawa rayuwar al’ummarmu muhimmanci. “in ji shi.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da yin iya kokarin ta don tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin gudanar da mulki wanda hakan ya sa jihar ta samu lambar yabo ta jihar da ta fi yin aiki a kan gaskiya da rikon amana a Najeriya daga bankin duniya wadda hakan ya taimaka wa jihar ta hanyar nuna gaskiya da kuma dorewa (SIFTAS).
“Ina da kwarin gwiwar cewa sabbin shugabannin hukumar kula da kudi ta Jiha, da hukumar kula da harajin cikin gida, za su yi aiki wajen inganta daidaito da sanin ya kamata wajen samar da kudaden shiga da kuma kashe kudaden gwamnati don inganta shugabanci nagari da samar da ingantacciyar hanyar hidima ga jama’a,” inji shi. .
Gwamnan ya bukaci sabon shugaban hukumar tara kudaden shiga na cikin gida Alhaji Suleiman Bakura da ya himmatu wajen inganta hanyoyin samar da kudaden shiga, tare da kuma tabbatar da shigar da dukkan kudaden shiga da aka tara a asusun gwamnati.
Buni ya kuma bukaci sabon shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jiha (SUBEB) Alhaji Babayo Umar da ya ba da himma ga kokarin gwamnati na ciyar da ilmi gaba ta hanyar tabbatar da ingancin koyo da koyarwa da samar da kayayyakin koyarwa da muhalli mai kyau.
“Ya kamata ku tabbatar da sa ido da kulawa mai inganci a makarantun, da kuma aiwatar da dukkan ayyukan da hukumar ta bayar.
Gwamnan ya kuma kaddamar da rabon tallafin tsabar kudi naira miliyan 50 da kayayyakin fara aiki ga mutane 500 da hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) da hadin gwiwar hukumar raya kasa ta majalisar dinkin duniya (UNDP) ta horar da su wajen samar da sabulu, sarrafa gawayi, takalma da magungunan kashe kwayoyin cuta.
Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun samu tallafin tsabar kudi naira 100,000 kowanne da kuma kayan fara aiki domin kaddamar da sana’o’insu domin samun dorewar samun kudin shiga, inda ya bukace su da su yi amfani da wannan damar domin samun kyakkyawar makoma.