Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya gabatar da jawabin karshen shekara ga ‘yan jarida a ranar alhamis, inda ya bayyana irin nasarorin da gwamnatin jihar ta samu a sassa daban-daban a wannan shekara ta 2024 da kuma bayyana tsare-tsare na gaba.
Buni wanda mataimakinsa Idi Barde Gubana ya wakilta ya yaba da kwazo da jajircewa da ‘yan jarida suka yi, inda ya yaba da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen sanar da jama’a irin ci gaban jihar ke samu karkashin mulkin dimukuradiyya.
Ya kuma ba su tabbacin gwamnati za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga kafafen yada labarai don gudanar da ayyukansu.
Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga ma’aikatan gwamnati da jami’an gwamnati bisa gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarorin da jihar ta samu a shekarar 2024.
Ya kuma bayyana cewa duk da kalubalen da ake fuskanta na tattalin arziki jihar ta sanya jari sosai a fannin kiwon lafiya, ilimi, noma, samar da arziki, da gina hanyoyi.
Ya bayyana cewa “Jihar Yobe ta samu dala 500,000 kan cigaban harkokin kiwon lafiya a matakin farko na jahohin yankin Arewa maso Gabas.
“A cewar sa Jihar ta kuma samu nasarar biyan 100% na alawus-alawus da kuma gyaran albashi na tsarin CONMESS da CONHESS na ma’aikatan lafiya don Inganta rayuwar jami’an bangaren.”
“Haka nan Jihar ta kaddamar da shirin tallafa wa aikin gona mafi girma, inda ta kashe zunzurutun kudi kimanin Naira biliyan 15.3 wajen samar da kayan amfanin gona ga manoma 5,340 a fadin mazabu 178 da ke Jihar.
“Gwamnati ta kuma sayo injunan dinki na zamani guda 475, ta raba nakasassu guda 350, sannan ta bayar da tallafin kudi ga kananan ‘yan kasuwa”.
Dangane da samar da ruwan sha kuwa jihar ta bayar da kwangilar sauya rijiyoyin burtsatse 170 zuwa tsarin masu amfani da hasken rana tare da hakar rijiyoyin burtsatse a manyan garuruwa yayin da ake aikin gina tituna a manyan garuruwan Jihar tare da gyara hanyoyin mota na daruruwan kilomitoci da suka hada da wadda ta tashi daga Damaturu zuwa Kalallawa da hanyar Gujba-Ngalda da sauran su.
Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar jihar Yobe cewa gwamnati za ta ci gaba da kokarin ganin an samar musu da rayuwa mai ma’ana a 2025 wajen gudanar da muhimman ayyukan raya kasa.
Ya jaddada muhimmancin karfafa tsaro da inganta rayuwar al’umma baki daya.
Jawabin Gwamnan ya kammala da yin kira ga duk masu ruwa da tsaki da su hada kai domin ci gaban jihar Yobe Baki daya.
Tun da farko da yake jawabi yayin jawabin maraba, Kwamishinan ma’aikatar harkokin cikin gida, watsa labarai da al’adu na Jihar Yobe, Abdullahi Bego, ya bayyana jin dadinsa ga taron manema labarai na karshen shekara.
“A madadin shuwagabanni da ma’aikatan ma’aikatar harkokin cikin gida da yada labarai da al’adu, ina mika godiya ta ga mai girma Gwamna Mai Mala Buni Chiroman Gujba, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa a koda yaushe Hon. Idi Barde Gubana wazirin Fune, saboda samun lokaci don yin jawabi ga wannan gagarumin taro na ‘yan jaridu da kafafen yada labarai na jihar mu.”
“Wannan shi ne karo na farko a cikin shekaru masu yawa da shi kansa Mai girma gwamna zai ba mu damar yin jawabi irin wannan taro na karshen shekara”.
“Ina kuma kara mika godiya ga mai girma Gwamna bisa irin ayyukan da yake ci gaba da yi a madadin al’ummar jihar wajen ciyar da al’amuran da gwamnatinsa ke yi a kodayaushe da suka hada da inganta rayuwar jama’a; tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin mutane; tare da hada ginshikan ginin da suka dace wadanda za su tabbatar da ci gaba da walwala ga al’ummar jihar nan gaba daya.
A madadin Mai Girma Gwamna da Gwamnatin Jihar Yobe, don haka ina mika godiyata ga daukacin membobin kungiyar ‘yan jarida na Jihar Yobe bisa hadin gwiwar da kuka yi da gwamnatin jihar tsawon shekaru da kuma abubuwan da kuke ci gaba da yi a matsayin masu ruwa da tsaki da kuma masu taka rawa wajen samar da zaman lafiya da tsaro da wadata a Yobe.