Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiƊangote Ya Ya Rage Farashin Mai a Najeriya

Ɗangote Ya Ya Rage Farashin Mai a Najeriya

Duba da halin kunci da al’umma ke ciki musamman a wanna lokaci, Matatar Dangote ta sake rage farashin mai

Kamfanin na Dangote ya dauki matakin ne duba da halin da ake ciki a Najeriya musamman a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara

Wannan ba shi ne karon farko ba da kamfanin ke rage farashin saboda a watan Nuwambar 2024 ma ya rage zuwa N970

Matatar mai na Aliko Dangote ta sake rage farashin man fetur a Najeriya yayin da aka fara bukukuwan karshen shekara.

Kamfanin ya rage farashin mai zuwa N899 kan kowace lita domin saukakawa al’umma a wannan lokaci.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da daraktan hulda da jama’a, Anthony Chiejina ya fitar a yau Alhamis 19 ga watan Disambar 2024, karamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kamfanin ya bayyana cewa matakin ya zama dole domin taimakawa ƴan Najeriya da sauƙin wahala a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

“Matatar mai a Afirka ta farko ta Dangote wanda ta rage farashin mai zuwa N970 a kowace lita a ranar 24 ga watan Nuwamba.”

“Yanzu ya sake sanar da sabon farashi na N899 a kowace lita.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments