Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya rantsar da sabbin sakatarorin dindindin da aka nada, da mambobin hukumar kula da ilimin bai daya na jihar, da shugabannin hukumomin kula da harkokin kudi da na kasafin kudi.
Taron rantsarwar wanda aka gudanar a dakin taro na Banquet dake gidan gwamnati dake Damaturu, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, da sauran masu ruwa da tsaki.
A nasa jawabin, Gwamna Buni ya taya wadanda aka nada murna, inda ya jaddada cewa nadin nasu ya dogara da cancanta, kwazo, da amana.
Ya bukace su da su inganta hadin kai da kuma gudanar da aiki tukuru, da fifita muradun jama’a fiye da na su.
Gwamnan ya kuma yi gargadi game da yin siyasa a shekarar 2027, inda ya bayyana cewa gwamnati ba za ta amince da duk wani abu da gangan na cin zarafi wajen fakewa da siyasa da nufin haifar da rudani ko karkatar da hankali daga mai da hankali ba.
Ya tunatar da sabbin jami’an gwamnati da aka rantsar da cewa rantsuwar aiki da suka yi an dora musu nauyi ne da ya kamata su yi hattara don ganin sun sauke wannan nauyi da ke kan su.
Sabbin Sakatarorin Dindindin da aka nada sun hada da Garba Hassan, Garba Tahir Usman, Mohammed Bello Saleh, da Shuaibu Baba Ahmed. An nada Goni Baba Gana Shugaban Hukumar Kula da Kudi, yayin da Babaji Dauda Galadima da Ali Koromari aka nada su mambobin dindindin a hukumar kula da kasafin kudi.
Bikin rantsar da jami’an na gwamnatin ya samu halartar mataimakin gwamna Hon. Idi Barde Gubana, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Chiroma Buba Mashio, da sauran manyan baki.