Saturday, April 26, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiNULGE Ta Bukaci A Biya Mambobin Ta Sabon Tsarin Albashi Daga Watan...

NULGE Ta Bukaci A Biya Mambobin Ta Sabon Tsarin Albashi Daga Watan Disamba A Jihar Yobe

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya NULGE reshen Jihar Yobe, ta nuna bukakar ta na a biya mafi karancin albashi na N70,000 ga mambobin ta, daga watan Disamba.

Shugaban kungiyar NULGE na jihar, Kwamared Baba Shehu Mustapha, ne ya bayyana haka, ne a Taron wakilan Kungiyar karo na 8 da aka gudanar a Damaturu, yadda ya ce, ma’aikatan kananan hukumomin sun yaba da amincewa da mafi karancin albashin ma’aikata da gwamnatin Jihar ta Yi, don haka ne suka bukaci suna a fara biyan su albashi daga wannan watan na Disamba 2024 kamar yadda ma’aikatan gwamnatin jihar aka alkawarta musu.

“Muna godiya da irin wannan karimcin da Mai Girma Gwamna Buni  ya yi na amincewa da mafi karancin albashi na 70,000 ga ma’aikatan jihar daga watan Disamba, 2024.

Haka kuma, muna fatan Gwamna Mai Mala Buni ya Yi irin  wannan karimcu ga ma’aikatan kananan hukumomin jihar.

“Wannan, idan aka yi la’akari da yadda muke zuwa kasuwa daya tare da ma’aikatan jihar kuma dukkanmu biyu masu tawali’u ne da ke fuskantar hauhawar farashin kayayyaki da ke fuskantar tattalin arzikin kasar,” in ji Baba Shehu.

Shugaban ya kuma bukaci gwamnati da ta kara kudin tafiyar da kananan hukumomi domin inganta gudanar da mulki na mataki na uku.

“Muna kuma rokon gwamnatin jihar da ta kara horar da ma’aikatan kananan hukumomi domin inganta ayyukansu,” inji shi.

Shugaban Kungiyar  ya ce NULGE za ta ci gaba da hada kai da gwamnati don ganin an samar da ingantacciyar hidima a matakin kananan hukumomi.

Ga ‘yan kungiyar, Baba Shehu ya ce kungiyar na yin kokarin ganin an tabbatar da karin girma ga ma’aikatan kananan hukumomin a kai a kai, tare da gaggauta biyan kudaden fansho da giratuti ga ma’aikatan kananan hukumomin da suka yi ritaya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments