Saturday, April 26, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeIlimiMun Sake Mayar Da Yara Kimanin 1.5m Makarantan Borno, inji Gwamna Zulum

Mun Sake Mayar Da Yara Kimanin 1.5m Makarantan Borno, inji Gwamna Zulum

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce gwamnatinsa ta mayar da yara sama da miliyan 1.5 zuwa makaranta.

Adadin ya nuna kashi 70% na yara miliyan 2.2 da ba sa zuwa makaranta a dukkan fadin  jihar ta Borno.

Gwamna Zulum ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin kaddamar da Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Mairi da Daraktan Bankin Duniya, Dr. Ndiame Diop ya yi.

Ya ce, a cikin shekaru biyar da suka gabata, gwamnatin ta dauki nauyin saka Kara habaka fannin ilimi ta wajen mayar da yaran ya zuwa makarantu  inda ya ce sauran yara 700,000 za a saka su a makarantu nan ba da dadewa ba da izinin Allah SWT.

“Mun gina makarantu kimanin 104, mun gyara ajujuwa 2,931, tare da raba kayayyakin ilimi kyauta, wadanda suka hada da littafan rubutu miliyan 20, litattafan karatu miliyan 2, uniform miliyan 15 na kayan makaranta, jakunkunan makaranta 700,000, da kuma miliyoyin kayayyakin koyo,” in ji gwamnan.

Ya kara da cewa shirin ciyar da daliban ya amfana da dalibai 50,000 a jihar, yayin da gwamnati ta kuma samar da kekuna 10,000 ga dalibai a yankunan karkara domin saukaka kalubalen sufuri.

Gwamna Zulum ya ce, wajen magance matsalar matasan da ba su zuwa makaranta da suka wuce shekarun karatu na al’ada, gwamnatin ta ba da fifiko kan ilimin fasaha da koyar da sana’o’i (TVET).

“Mun kafa Cibiyoyin Sana’o’i guda biyar, Makarantun Sana’o’i na Mata/Yan Mata biyu, sannan mun sake farfado da Cibiyoyin Koyar da Sana’o’i guda tara.

“Manufarmu ita ce horar da masu sana’a kusan 5,000 a duk shekara, tare da ba su karfin gwiwa don dogaro da kai da magance kalubalen rashin aikin yi.”

A nasa jawabin, Daraktan Bankin Duniya Dr Diop ya yaba da kudurin jihar Borno na sake gina fannin ilimi, inda ya bayyana cewa bankin ya tallafawa gina makarantun sakandire 41 da kuma gyara makarantu 392 a fadin jihar.

“Wannan makaranta alama ce ta kokarin gwamnatin Borno wajen sake ginawa duk da halin rashin tsaron da aka yi fama da shi  Kokarin da jihar ke yi ya burge mu kuma za mu ci gaba da  tallafa wa manufofin Gwamna Zulum,” in ji Diop.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments