Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnatin jihar Yobe ta hannun ma’aikatar samar da arziki, karfafawa da samar da ayyukan yi ta bayar da tallafin babura kimanin 350 ga nakasassu a jihar.
Shugabar kwamitin shirya taron bada tallafin , Fatima Mohammed Faga ce ta mika tallafin a madadin ma’aikatar ga shugaban kungiyar nakasassu ta kasa (JONAPWD) Usman Bura a yayin bikin ranar nakasassu ta duniya ta 2024.
Taron mai taken, “Shugabanci domin Samun cigaba maɗaukaki” wanda asusun tallafawa al’umma na majalisar dinkin duniya (UNPFA) ya gudanar a Damaturu wanda ya sami halartar masu ruwa da tsaki, abokan ci gaba, jami’an tsaro da nakasassu.
Har ila yau, a wajen bikin, wata kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa, (Care International) ta kuma ba da gudummawar kayayyakin tallafi ga adadin nakasassu 100.
A jawabinta na maraba, Fatima ta nanata kudurin gwamnati da abokan ci gaba na bunkasa hada-hadar nakasassu.
A cewarta, “Wannan shirin yana nuna kudurinmu na hadin gwiwa don tabbatar da cewa nakasassu sun kai ga gaci.”
A nasa jawabin, Mista Oghene Tega, jami’in kula da sashen nakasassu (DWG), ya bayyana cewa kawo yanzu suna iya tattara bayanan nakasassu a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.
“Yanzu muna da kusan kashi 60 na bayanan nakasassu a jihohin BAY,” in ji ta.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban kungiyar nakasassu ta kasa (JONAPWD) Usman Bura Gabai, ya bukaci gwamnatin jihar da ta amince da kudirin nakasassu a jihar, inda ya bayyana shi a matsayin abu mai muhimmanci wajen kare hakkin nakasassu”.
Haka kuma, ‘yan kungiyar nakasassu sun nuna godiya ga gwamnatin jihar da sauran masu hannu da shuni kan abubuwan da aka basu tare da yin alkawarin yin amfani da su yadda ya kamata.