Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnatin Borno ta raba N987m ga ‘yan kasuwa 7,716 wadanda bala’in ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri ranar 10 ga watan Satumba.
Injiniya Baba Gujbawu, shugaban kwamitin raba kudaden tallafin da bala’o’in ambaliyar ruwa, ya bayyana hakan a wajen bikin bayar da takardar shaidar tantancewar da aka yi a Maiduguri.
Gujbawu ya ce kwamitin ya shafe watanni biyu yana tantance tare da raba kayan agaji ga gidaje da abin ya shafa a kananan hukumomin Maiduguri, Jere, da Mafa da kuma ‘yan kasuwa daga manyan kasuwanni tara na jihar.
Ya ce kasuwannin da abin ya shafa sun hada da Kasuwar Gamboru, Kasuwar Monday, Tashan Damboa, Metro Plaza, El-kanemi, Kasuwar Kayan lambu, Kasuwar Kwastam, Kasuwar Ganye ta Moromoro, Bukar Shuibu, da Kasuwar Budum.
Ya bayyana cewa an ware wadanda suka ci gajiyar tallafin ne bisa la’akari da irin barnar da aka samu a kasuwancinsu, wanda ya hada da wadanda suka rasa komai da kuma wadanda kadan ya shafa, inda ya kara da cewa za a shigar da kudaden ne kai tsaye zuwa asusun ajiyar ‘yan kasuwar.
Don haka ya bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da kudaden cikin adalci wajen sake ginawa da fadada kasuwancinsu.
Wakilinmu ya ruwaito cewa kwamitin ya kuma mika injinan famfun ruwa guda 500 ga manoman da bala’in ya shafa a kananan hukumomin Maiduguri da Jere.
Alhaji Bawu Musami kwamishinan noma wanda ya karbi famfunan ruwan a madadin manoman ya bada tabbacin cewa za’a raba kayan cikin gaggawa ga wadanda suka ci gajiyar shirin noman rani.
Babban abin da ya fi daukar hankali a wajen bikin shi ne gabatar da takardar kudi ga babban Manajan kasuwar Maiduguri, wacce aka fi sani da kasuwar Litinin da shugaban kwamitin ya yi.