Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Hukumar kidaya ta kasa (NPC) ta ce, binciken da ake yi na 2024 na Verbal and Social Autopsy Studies (VASA) ya ba da muhimman bayanai da suka taimaka wajen tsara manufofin kiwon lafiya da shiga tsakani da nufin rage mace-macen kananan yara da mata ma su juna biyu a Najeriya.
Kwamishinan hukumar ta NPC na Jihohin Borno da Yobe Barista Isa Audu Buratai ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin bikin kaddamar da gangamin nazarin kididdigar yawaitar mace-mata yara kanana da masu juna biyu (VASA) na shekarar 2024 a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Buratai ya ce, binciken na (VASA) ya zo ne tun daga shekarar 2023 zuwa 2024 da aka kammala a watan Mayun bana.
Ya bayyana cewa, binciken zai hada da tuntubar magidanta NDHSa don neman bayanan da za su taimaka wa gwamnati ta fahimta da kuma tsara yadda za a magance matsalolin da ke haifar da mutuwar yara ‘yan kasa da shekara 5 da kuma mata masu juna biyu.
“A jihar Yobe, mun ci gajiyar hadin gwiwa mai karfi tsakanin hukumar Kidaya (NPC) da ma’aikatar lafiya ta tarayya (FMOH) da abokan huldar mu wajen samun nasarar aiwatar da ayyukan da suka shafi kiwon lafiya a baya , kuma muna da yakinin cewa wannan hadin gwiwa zai sake tabbatar da samun nasara. VASA”, in ji Kwamishinan NPC Yobe da Borno.
Ya kuma bayyana cewa, za a gudanar da aikin binciken ne a zababbun wurare da ke cikin al’ummomin Jihar ta Yobe a tsakanin ranakun 4 ga Nuwamba zuwa 15 ga Disamba 2024.
Buratai ya yi kira ga shugabannin al’umma da su jajirce wajen nuna goyon bayansu ga binciken, tare da karfafa gwiwar al’ummarsu da su yi maraba da jami’an da aka turo dom ganawa da su kan wannan kudiri.
A cewarsa ta yin hakan ne za’a samu ainihin kudirin da ake so a Cimma wadda hakan zai taimaka matuka wajen samo bakin zaren magance wannan babbar matsala ta yawaitar mace-macen kananan yara da mata masu juna biyu da ake samu akai-akai.
Kwamishinan ya ci gaba da cewar kan wannan babban lamari ne hukumar su ta kidaye ke iya kokarin ta wajen samo ainihin hanyoyin magance wannan matsala ta hanyar tura jami’an ta ko’ina a wannan yanki musamman jihohin Yobe da Borno kowane lungu duk da kalubalen tsaro da ake fuskanta don binciken kwakwaf.