Daga, Sani Gazas Chinade , Damaturu
Uwargidan gwamnan jihar Borno, Dr. Falmata Babagana Umara Zulum tare da hadin gwiwar ma’aikatar mata ta Jihar sun gudanar da bikin ranar nakasassu ta duniya tare da kaddamar da rabon kayayyakin tallafi ga nakasassu.
Taron wanda ya gudana a dakin taro na Multi-Purpose Hall dake gidan gwamnati a Maiduguri yadda uwargidan gwamnan na Borno ta raba kayan tallafi ga nakasassu 400 da suka hada da matasa maza da mata da yara.
Uwargidan gwamnan jihar Borno a hukumance ta kaddamar da rabon kayan tallafin ga nakasassu 400 wadanda suka hada da injinan dinki 100, injin nika 40, kayan alfarma 200, da suka kunshi turaren wuta, da tallafin kudi na Naira 10,000 kowannensu ga mutum 60.
Ta ce an yi wannan kokarin ne domin inganta ‘yancin nakasassu da kuma inganta rayuwar nakasassu masu a Jihar.
Tun da farko a jawabinta na maraba, kwamishiniyar ma’aikatar mata da ci gaban jama’a ta jihar Borno, Hon. Zuwaira Gambo ta jaddada kudirin gwamnatin jihar Borno da sadaukar da kai na tallafa wa nakasassu tare da jinjinawa irin jagorancin da Jihar ke da shi karkashin gwamna Zulum.
Wasu jigogin kungiyoyin Nakasassu da suka hada da da Modu Mustapha Adamu Gaji da Kwamared Bulama Abiso, Babban Daraktan CSOs na yankin arewa maso Gabas, wadanda suka bayyana godiyar su bisa wannan karamci na gwamnatin jihar Borno kan kokarin da take yi na inganta rayuwar mambobin su.
Biyu daga cikin mutanen da suka ci gajiyar tallafin, Ahmadu Umar da Mohammed Abubakar, suma sun bayyana jin dadinsu yayin da suke godewa kwamishinar ma’aikatar mata Dr. Zulum Gambo da ma’aikatar bisa gagarumin tallafin da suka bayar.
A nasa jawabin babban sakataren ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma, Alhaji Mohammed Hamza, ya yabawa masu ruwa da tsaki na Jihar bisa ga irin wannan kokari tare da bayyana kwarin guiwar cewa, shirin zai kara inganta rayuwar nakasassu a jihar Borno.