Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeIlimiAn bayyana Matakin ilimin shine ginshiki cigaban dukkanin alumma

An bayyana Matakin ilimin shine ginshiki cigaban dukkanin alumma

Daga Rabiu Sanusi

Shugaban karamar Hukumar Ungogo Alhaji Tijjani Amiru Bilyamu ya tabbatar dacewa ilimin shine ginshiki cigaban dukkanin alumma cikin hanzari ta wace fuska.

Wannan batu ya biyone a daidai lokacin wata mahimmayar ganawa da aka gudunar da Jin ra’ayoyi a tsakanin Shugaban Makarantun firamare Wanda aka shirya shi a cibiyar yada addinin muslunci yankin.

Alhaji Tijjani Amiru Bilyamu Wanda ya Sami wakilcin kansilar ilimin yankin Abdullahi Wakili yayi Karin haske tare da bayyana mahimmanci koyar da Karatun a tsakanin Dalibai da alumma baki daya .

Ainda ya tabbatar da Majalisar karamar hukumar zata cigaba da bada fifiko wajen cigaban Samar da kayyakin koyo da koyarwa a dukkanin makarantu yankin baki daya.

Shugaban ya tabbatar da dacewar za su hada hannu da kungiyoyin masu zaman kansu wajen cigaban harkokin ilimin yankin.

A sakon sa Shugaban karamar Hukumar Alhaji Tijjani Amiru Bilyamu ya jinjawa Gwamnatin Jahar Kano a karkashin Abba Kabir Yusuf yadda yake nuna damuwar sa wajen cigaban harkokin ilimin a kana nan hukumomi 44 dake Jaha..

Daya daga cikin Malam Alhaji Shehu ya daukin alkawarin bada cikkaken goyon baya da tsare tsaren gwamnatin Mai ci ayanzu domin cigaban harkokin koyo da koyarwa da suka dauki alkwarin yin sa .

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments