Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiHatsarin mota ya Lakume Rayukan Mutane 12 A  YOBE-FRSC

Hatsarin mota ya Lakume Rayukan Mutane 12 A  YOBE-FRSC

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Kimanin Mutane 12 da suka hada da maza 10, mata biyu ne suka rasa rayukan su sakamakon  wani hatsarin mota da aka yi  a ranar Talata, 3 ga Disamba, 2024 akan titin Baimari zuwa Geidam a jihar Yobe.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra (FRSC) reshen jihar Yobe,  Corps LIVINUS YILZOOM ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a garin Damaturu.

A cewarsa, hatsarin ya afku ne da misalin karfe 10:00 na dare a kilomita 20 daga garin na Gaidam gab da  kauyen CHELLURI dake kan titin na Baimari-Geidam.

Ya kuma bayyana cewa hatsarin ya rutsa da wata babbar mota kirar Howo dake tsaye mai lamba: MAG831ZR mallakin kamfanin DAN NENE Construction da wata karamar Bus Sharon mai lamba: BAU124YF, wadda ta shiga cikin babbar motar wadda nan take ta kama wuta, inda ta kone mutane 12 da ke cikin motar Sharon din kurmus.

A cewar Mista Yilzoom, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa babbar motar ta HOWO ce ta kawo cikas a kan hanya, yayin da direban Sharan din ke tafe a guje da ba zai yiwu ya iya sarrafa motar ba don kaucewa afkawa babbar motar da ke tsaye.

Ya kuma gargadi masu ababen hawa da su guji tafiye-tafiyen dare saboda hadarin rashin ganin abin da ke gaban direba kamar yadda ya kamata musamman a wannan lokaci na hunturu da aka yawaitar samun hazo

Ya yi kira ga masu ababen hawa da su rika bin ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa a kowane lokaci domin dakile afkuwar lamarin nan gaba.

Daga karshe ya mika ta’aziyyar Babban shugaban hukumar ta (FRSC)Marshal Shehu Mohammed,  ga iyalan wadanda suka rasu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments