Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiZulum Ya Bukaci A Fadada Tuntuba Akan Gyaran Haraji Na (VAT) Don...

Zulum Ya Bukaci A Fadada Tuntuba Akan Gyaran Haraji Na (VAT) Don Kaucewa Kitso Da Kwarkwata

***Bana adawa da Gwamnatin Tinubu

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kira da a kara yin tuntuba kan kudirin sake fasalin haraji da majalisar dokoki ta kasa ke nazari a kai.

A cikin wata sanarwa da Dauda Iliya  kakakin Gwamna Zulum kuma Mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ya ce, gwamnan ya fadi haka ne a cikin jawabin sa a  wani shirin gidan Talabijin na Channels TV mai suna “Sunday Politics”, ya jaddada muhimmancin tattaunawa da masu ruwa da tsaki don magance matsalolin da rashin fahimta da ke tattare da kudirin.

“Shawarwari babban jigo ne a tsarin dimokuradiyya,” in ji Gwamna Zulum. “Dole ne mu dauki lokaci don fahimtar da al’ummar mu abubuwan da ke cikin kudirin da kuma tabbatar da cewa an kawar da duk wuraren da ake takaddama kafin aiwatarwa.”

Gwamnan ya nuna damuwarsa ta musamman game da tanadin da aka ware kashi 60% na haraji (VAT) bisa la’akari da abin da tsarin da ake kai yanzu.

Ya yi gargadin cewa idan har an aiwatar, zai amfanar da jihohin Legas da Ribas ne kawai, abin da zai iya jefa sauran jihohin cikin mawuyacin hali.

“Tsarin na VAT, kamar yadda aka tsara a halin yanzu, ya nuna cewa jihohi kalilan ne za su amfana sosai,” Gwamna Zulum ya bayyana. “Wannan shine dalilin da ya sa bai kamata mu hanzarta aiwatar da tsarin ba, manufar ita ce tabbatar da adalci.”

Gwamna Zulum ya kuma ba da shawarar cewa, a yi garambawul ga abubuwan da ke haifar da cece-kuce a cikin kudirin da ka iya kawo cikas ga ci gaban kasa, yana mai jaddada bukatar daidaita tsarin.

“Ba Na adawa da Gwamnatin Shugaba Tinubu”

Gwamna Zulum ya yi watsi da kalaman batanci da ke nuna yana adawa da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya fayyace cewa kalaman nasa yayi ne don bayar da shawarar samar da hanyar da ta dace ga kudirin da aka gabatar.

“Akwai kuskuren cewa Arewa na adawa da Shugaban kasa,” inji Zulum. “Wannan ba gaskiya bane, Arewa ta bayar da kashi 60.2% na kuri’unsa, wanda hakan ke nuna goyon bayanmu, kirana ga shugaban kasa shi ne ya yi la’akari da kalubalen da wasu Jihohi ke fuskanta, ya yi kokarin ganin an magance matsalolin da za su amfanar da kasa baki daya.

Dangane da Ci gaban Noma a Jihar Borno kuma Gwamna Zulum ya bayyana irin matakan da gwamnatinsa ke daukawa na bunkasa noman rani na zamani, da nufin samar da abinci a yankunan Damasak, Baga, da sauran sassan jihar Borno.

“A karshen wa’adina, Borno za ta kasance mai fitar da kayan amfanin gona kamar shinkafa, alkama, dawa, da masara,” in ji Gwamnan.

Ya bayyana cewa, an noma gonakin shinkafa mai tsawon kilomita 16 a Damasak, yankin da ‘yan tada kayar baya suka taba yin mummunar barna.

Zulum ya kara da cewa, “An samu wannan ci gaba ta hanyar goyon bayan gwamnatin tarayya da hadin gwiwa da sojoji, wanda hakan ya sa aka samu yabanya mai yawa a bana.”

Ya sanar da samar da kayan masarufi da takin zamani na Gwamnatin Tarayya, wanda ya kara karfafa ayyukan noma.

Gwamnan ya kuma bayyana godiyarsa ga sojoji, Civilian Joint Task Force (JTF), mafarauta, ’yan banga, da jajirtattun al’ummar jihar Borno bisa kokarin da suke yi na maido da zaman lafiya.

“Ta’addancin Borno ya ragu da kusan kashi 90%,” in ji shi. “Wannan nasarar ta shaida kwazo da jajircewar jami’an tsaron mu da kuma jajircewar ‘yan kasarmu.

 

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments