Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaSahihin Zaben Kananan hukumomi Aka Yi A Jihar Yobe Inji Shugaban IPAC 

Sahihin Zaben Kananan hukumomi Aka Yi A Jihar Yobe Inji Shugaban IPAC 

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Majalisar ba da shawara ta jam’iyyar Inter Party (IPAC), reshen jihar Yobe, ta ce, zaben kananan hukumomin jihar Yobe da aka gudanar a watannin baya, an gudanar shi ne bisa gaskiya da adalci wadda aka aminta da sahihancin sa.

Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Shugaban hadakar jam’iyyum siyasar Jihar (IPAC) Umar Adamu Jajere wanda ya bayyana hakan a Damaturu, babban birnin jihar Yobe don kalubalantar shugaban jam’iyar ADC  da ke kokarin cewar, ba’a gudanar da zaben kananan hukumomi mai sahihancin ba a Jihar.

Ya kuma bayyana zaben a matsayin wanda aka gudanar da shi cikin adalci a tarihin jihar, inda ya fara da cewa masu zabe sun gudanar da zabe yadda ya kamata duk da irin halin da ake ciki a siyasance.

Jajere ya ce, zabukan kananan hukumomin da aka gudanar a fadin kananan hukumomi 17 na jihar tsakanin watan Mayu zuwa Yuni na 2024 ya kasance daya daga cikin zabukan da suka fi inganci a tarihin jihar.

A cewarsa, zaben kananan hukumomin an gudanar da shi cikin gaskiya da adalci, yana mai cewa ba a yi taho-mu-gama ba a kananan hukumomi 17 kuma kowa yana gudanar da aikinsa cikin lumana na tare da tsangwama ba.

Ya kara da cewa, “Ina so in gaya muku cewa, zaben ya kasance mai karbuwa a duk jam’iyyun siyasa da suka shiga  zaben domin wannan shi ne jigon jam’iyyar siyasa.”

Don haka ya bukaci sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomi 17 da su gudanarwa ayyukan da al’umma su za su San cewar lalle sun ci ribar dimokuradiyya a matakin farko.

Zaben ya kare, kuma yanzu ku ne shugabanni ga kowa.  Ku kasance masu adalci ga kowa, kuma a mai da hankali wajen isar da ci gaba a kowane lungu na jihar

“A matsayinku na kurkusa da gwamnati, ana sa ran ku tsara manufofi da aiwatar da tsare-tsare masu tasiri da inganta rayuwar al’umma a kananan hukumomin ku.

Allah ya zaɓe ka don wannan alhakin, ba don ka fi wasu ba, amma don yana faranta masa rai.  Yi amfani da wannan damar don yin hidima ga al’ummar ka.

Ya yabawa gwamnan jihar Mai Mala Buni da hukumomin tsaro da masu rike da mukaman jihar da sauran jam’iyyun siyasa bisa goyon bayan da suke baiwa jama’a wajen zabar shugabanninsu a matakin farko.

“Zaben ya kasance cikin gaskiya, da adalci, wadda muka yi farin ciki da sakamakon.  “Na yi imanin cewa kowa ma ya ji dadin hakan, mun gana da daukacin mambobinmu na IPAC kuma mun amince da sakamakon zaben kafin a sanar da shi.” Inji Jajere.

Shugaban yayin da yake mayar da martani ga wata sanarwa ta kage da aka yi a shafukan sada zumunta na cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Yobe ta soke zaben kananan hukumomi.

Shugaban IPAC na jihar ya ce labarin zance  ne gaba kawai don an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci yadda jam’iyyun da suka shiga zaben qakilan su suka aminta da sahihancin zaben.

Shugaban IPAC ya yi kira ga daukacin al’ummar Yobe da su yi watsi da wannan da’awar da aka yi, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum cikin nutsuwa tare da yin watsi da masu wancan ra’ayin da ba shi da kamshin gaskiya tattare da shi.

Umar Jajere ya bayyana cewa,  a Jihar Yobe IPAC ta ci gaba da jajircewa wajen ingantawa da kare hakki da muradun al’ummar Jihar don samar da dimukuradiyya mai cike da qalwala da sanin ya kamata.

Ya bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan da labaran karya, sannan a rika tantance bayanai ta hanyar sahihiyar majiya kafin a raba su ga al’umma don gudun shiga rudani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments