Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiNoma Ya Bunkasa Duk Da Kalubalan Tsaro A Jihar Borno inji Gwamna...

Noma Ya Bunkasa Duk Da Kalubalan Tsaro A Jihar Borno inji Gwamna Zulum 

Sani Gazas Chinade Daga, Maiduguri

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewar, an samu matukar cigaba a harkokin aikin noma a Jihar duk da kalubalen tsaro da suka rika fama da shi na tsawon lokaci.

Kamar yadda kakakin Gwamnan Dauda Iliya ya ambata cewar Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a cikin tattaunawar sa da tashar talabijin ta Channel yadda ya ce, irin matakan da gwamnatinsa ke dauka na bunkasa noman rani na zamani, da nufin samar da abinci a yankunan Damasak, Baga, da sauran sassan jihar Borno wadda yankuna ne da suka shahara tun fill-azal kan harkokin noma musamman noman rani.

“A karshen wa’adina, Borno za ta kasance mai fitar da kayan amfanin gona kamar shinkafa, alkama, dawa, da masara,” in ji Gwamnan.

Ya bayyana cewa a bana kadai an noma gonakin shinkafa mai tsawon kilomita 16 a Damasak, yankin da ‘yan tada kayar baya suka taba yin mummunar barna.

Wannan hobbasa na manoma a wadannan yankuna na Damasak, Baga, da sauran yankunan Jihar wajen cigaba da noman rani ya sa Jihar Borno in Allah ya so za ta kwato kambun ta wajen kan gaba wajen samar da abinci a arewa da ma Sauran yankunan kasar nan musamman ta fuskar samar da cimaka wadda hakan ba ta samu ba sai tare da taimakon Allah SWT da Kuma jajircewar jami’an tsaron mu wajen samar da zaman lafiya.

Zulum ya kara da cewa, “An samu wannan ci gaba ta hanyar goyon bayan gwamnatin tarayya da hadin gwiwa da sojoji, wanda hakan ya sa aka samu yabanya mai yawa a bana.”

Ya sanar da samar da kayan masarufi da takin zamani na Gwamnatin tarayya, wanda ya kara karfafa ayyukan noma a yankunan da aka ambata.

Kan hakan ne ma Gwamnan ya nuna godiyarsa ga sojoji, Civilian Joint Task Force (JTF), mafarauta, ’yan banga, da jajirtattun al’ummar jihar Borno bisa kokarin da suke yi na maido da zaman lafiya a Jihar har ma ta Kai ga manoma suka Ci gaba da harkokin su na noma sabanin a shekarun baya da lamura suka rikici yadda noman ya gagara sakamakon rikicin masu tada kayar baya.

“A cewar sa ta’addancin Borno ya ragu da kusan kashi 90%,” in ji shi. “Wannan nasarar ta shaida kwazo da jajircewar jami’an tsaron mu da kuma jajircewar ‘yan kasarmu.”

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments