Daga RABIU SANUSI a Kano
Shugaban Hukumar Dakile yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki da akafi sani da(AIDs) Dr. Usman Bashir ya bayyana cewa an kwashe shekara biyu(2) ba’ayi gwajin cutar ba a jihar Kano.
Dr.Bashir Usman ya bayyana haka ne a yayin gudanar da bikin tinawa da ranar masu cuta mai karya garkuwar Jiki da Majalisar dinkin duniya ta fitar.
shugaban hukumar ya tabbatar ma da manema Labarai cewa idan zasu iya tunawa gwamnatin da ta gabata tayi watsi da masu wannan cuta ta hanyar rashin hakin ko in kula da ta bayyana wajen basu damar gwajin wannan cuta dan Daukar matakin da ya dace dasu.
”A yanzu haka zuwan gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf sai da ta bamu kudu kashi biyu na farko naira milyan(60,000) mun sayi kayan aiki na gwaje-gwaje tare da sayen abinda yakamata.
sannan ya kara da cewa daga bisani kuma gwamnann ya kuma kara tabbatar da baiwa wannan hukuma naira milyan(90,000) dan kara inganta ayukan hukumar da kayan aiki.
”haka kuma yanzu haka akwai asibitoci guda a kananan hukumomi 43 da ake gwada masu wannan matsalar a fadin jihar Kano kuma ana yin Nasara sosai.
”Muna kokarin wayar ma da Al’ummar jihar Kano kansu ta hanyar shirye-shiryen mu a gidajen Rediyo da Talabijin harma da sauran Jaridu da kafafen sadarwa na zamani kuma abin nayin Tasiri matuka.
DG SACA ya kuma bukaci Jama’ar Kano da su kokarta sanin kansu wajen yadda zasu je wajen inda za’ayi masu gwajin cutar batare da fuskantar matsaloli ko tsangwama ba.
”Yanzu haka muna hada kai da sauran kungiyoyin da suke da nasaba da Bangaren lafiya wajen kara shiga lungu da sako wajen wayar da kan Jama’a,wani lokacin ma akwai masu dauke da cutar bangaren mata dasu ake shiga wajen wayar da kan Al’ummar mu.
Dr Usman yace kusan taken ranar na wannan karon shine ”Ba’asan haihuwar yaro da cuta mai karya Garkuwar Jiki.”In ji Dr Usman.