Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamna Farfesa Babagana Umara Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa mutane daban-daban da suka hada da sojoji da fararen hula na cin gajiyar tashe tashen hankula da ke faruwa a yankin.
Gwamna Zulum ya bayyana haka ne a yayin wani taron manema labarai na baya-bayan nan da aka gudanar a Maiduguri babban birnin Jihar, yadda ya jaddada cewa wadannan da suka ci gajiyar wannan rikici ba su da niyyar warware shi, yana mai bayyana irin alakar da ke tsakanin masu ba da labari na cikin gida da masu tayar da kayar baya.
Gwamna Zulum ya kuma yi nuni da irin kalubalen da ke tattare da kutse daga kasashen waje da kuma raunin kan iyakoki, musamman a kewayen tafkin Chadi da dajin Sambisa, wadanda ke ruruta ayyukan ta’addanci.
Daga nan Gwamnnan sai ya kirayi al’ummar Jihar Borno da ma na dukkan sassan Tafkin Chadi da su cigaba da dukufar addu’ar Allah SWT ya Yi raga-raga da masu goya baya ga wannan rikici na masu tada kayar baya, tare da addu’ar Allah ya kawo karshen lamarin.