Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Buni Ya Gwangwaje Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Da Kananan 'Yan Kasuwa...

Gwamna Buni Ya Gwangwaje Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Da Kananan ‘Yan Kasuwa Da N2.93

Daga, Sani Gazas Chinade Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya kaddamar da bayar da tallafin naira biliyan 2.93 ga mutane 40,000 wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da kuma kananan ‘yan kasuwa a jihar don Kara jari.

Gwamnan  ya bayyana hakan ne a babban dakin taro na gidan gwamnatin da ke garin Damaturu, yadda ya  ce, mutane  25,000 daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi su ne wadanda  ambaliyar ruwa a shekara ta 2024 ta shafa da kuma marasa galihu, yayin da wasu 15,000 kuma kananan ‘yan kasuwa ne.

“Ya kara bayyana cewa manufar wannan taron shine kaddamar da gabatar da shirye-shiryen tallafin gwamnatin jihar don karfafawa ‘yan Jihar mu da suka hadu da Iftila’in ambaliyar ruwan da kuma taimakawa kananan ‘yan kasuwar mu don su kara habaka harkokin su na kasuwa.”

“Kamar yadda kuka sani, jihar Yobe ta sami ambaliyar ruwa da ba a taba ganin irinta ba tsakanin watannin Afrilu da Oktoba na wannan shekara ta 2024 wadda   kimanin al’ummomi 441 a fadin kananan hukumomi 17 ne abin ya shafa, inda sama da magidanta 20,000 suka rasa matsugunansu.”

“Abin bakin ciki, mun rasa rayuka 34 sakamakon ambaliyar ruwa, wasu 386 kuma suka jikkata, sannan sama da mutane 50,000 sun rasa hanyoyin rayuwa,” in ji shi.

“Gwamnan ya ce kowane daya daga cikin mutane 25,000 da ambaliyar ruwa ta shafa da marasa galihu za su samu tallafin Naira 50,000, yayin da aka ware Naira 100,000 ga kowanne daga cikin kananan ‘yan kasuwar mu su kimanin 15,000.”

Buni ya ce gwamnatinsa ta gyara muhimman hanyoyin da ambaliyar ruwa ta lalata, da suka hada da Damaturu-Bayamari, Kariyari, Jumbam, Koromari-Bayamari, Geidam-Bukarti, Katarko-Gujba, da Tarajim.

Ya ce, gwamnatin tarayya, da abokan huldar mu sun raba tsabar kudi naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ta shafa baya ga kayan abinci da da aka raba tun da farko a yankunan da lamarin ya fi kamari.

“Wadannan tsare-tsare suna nuna ka’idojin gudanarwa na gwamnatinmu don tallafawa marasa galihu, karfafawa ‘yan kasarmu, da samar da hanyoyin dogaro da kai da wadata.”

Ya yaba da jajircewar al’ummar Jihar da kuma sadaukar da kai da hukumomin gwamnati daban-daban suke yi ba tare da gajiyawa ba wajen bayar da tallafi ga jama’a.

Buni ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma abokan ci gaban kasa da kasa da na cikin gida bisa goyon bayan da suke baiwa jihar ta kowace fuska yayin da bukatar hakan ta taso.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments