Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Kungiyar Kwadago ta kasa NLC reshen Jihar Jihar ta bada sanarwar nesanta kanta da Wata sanarwar da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani, wadda ke kira ga ma’aikatan jihar Yobe da su shiga yajin aikin gama gari daga ranar 1 ga watan Disamba da cewar wannan labarin karya ne marar tushe.
A wata sanarwa da wakilinmu ya samu yau asabar dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta NLC reshen jihar Yobe, Muktar Musa Tarbutu, na cewa kwamitin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da NLC ya kammala tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi, kuma an mika rahoton ga gwamna Mai Mala Buni don neman sahalewar sa.
Dom haka kungiyar kwadagon NLC ta bukaci daukacin ma’aikatan jihar Yobe da su yi watsi da wannan sanarwa ta bogi su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
An kuma gargadi jama’a da su yi taka-tsan-tsan da yada labaran karya tare da tantance labari kafin a yada shi
Kungiyar NLC ta jihar Yobe za ta ci gaba da jajircewa wajen ingantawa da kare hakki da muradun ma’aikatan jihar Yobe.