Daga, Sani Gazas Chinade , Maiduguri
Gwamnatin jihar Borno ta bayar da tallafin babura 18 na sintiri ga dakarun runduna ta 25 dake karamar hukumar Damboa a Jihar domin bunkasa ayyukansu kan harkokin tsaron yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram.
Da yake gabatar da baburan a wajen wani biki a Maiduguri, Kwamishinan yada labarai da harkokin tsaron cikin gida na Borno, Farfesa Usman Tar, ya ce an dauki matakin ne domin karfafa gwiwar kokarin da rundunar sojojin da ke aikin yakar ‘yan ta’adda a karkashin Operation Hadin kai ke yi.
Mista Tar, wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar, Modu Mustapha, ya ce gwamnatin jihar na da dadadden tarihi wajen tallafawa ayyukan soji a jihar.
Ya ce tallafin da aka baiwa sojoji a baya sun hada da motoci kirar hilux, na’urorin sa ido, man fetur, da manyan injuna irin su na’urorin zamani hade da motocin taimakawa wajen yakar ‘yan ta’addan.
Da yake karbar baburan a madadin sojoji, kwamandan runduna ta 25, Birgediya Janar Rasheed Omolori, ya mika godiyarsa ga Gwamna Zulum da al’ummar Borno bisa goyon bayan da suke bai wa sojoji.
“Wadannan babura za su haɓaka ikonmu na fuskantar abokan gaba da sauri ba tare da bata lokaci ba a duk yayin da hakan ta taso.
“A madadin kwamandan rundunar ta OPHK, Manjo Janar Waidi Shuaibu, na amince da karba tare da tabbatar wa gwamnati da jama’ar Borno cewa za a yi amfani da su yadda ya kamata wajen yaki da ayyukan tsaro,” in ji Mista Omolori.