Daga, Sani Saleh Chinade, Damaturu
Gwamna Babagana Umara Zulum, ya amince da karin albashi ga likitocin da ke aiki a ma’aikatan gwamnatin Jihar don karfafa musu cigaba da aiki a Jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a Wani taron da aka gudanar kan harkokin kiwon lafiya karo na 65 da a Maiduguri mai take da harshen turanci, ‘(Accelerating Pathway to Universal Health Coverage Strategies for 2030’.)
Zulum ya umurci shugaban ma’aikata na jihar da kwamishinan lafiya da su hada kai da hukumomin gwamnatin tarayya da abin ya shafa domin a daidaita matsalar albashin likitocin.
Don haka gwamnan ya ba da umarnin aiwatar da hakan daga ranar 1 ga Disambar wannan shekara ta 2024.
“Aiwatar da albashi iri daya da na likitocin da ke aiki a gwamnatin tarayya kan karin albashin likitocin don tabbatar da cewa babu bambance-bambance tsakanin albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya da masu aiki da gwamnatin jihar shine mafi zama fa’ida a wannan lokaci da ake ciki,” in ji Zulum.
“Ya zuwa ranar 1 ga watan Disamba, likitocin da ke aiki da gwamnatin jihar Borno za su karbi albashi daidai da wanda ke aiki da gwamnatin tarayya in Allah ya so.”
Gwamnan ya kuma bayyana cewa tun tunin jihar Borno ta bi dokar gwamnatin tarayya da ta bukaci kowace jiha ta tarayya ta ware akalla kashi 15 na kasafin kudinta na shekara domin kula da lafiya.
“Ina alfaharin bayyana cewa jihar Borno ta dauki muhimman matakai wajen cimma kudirin gwamnatin tarayya a cikin kasafin kudinmu na baya-bayan nan yadda muka ba da fifiko kan ababen more rayuwa na kiwon lafiya, da kara samun damar kula da lafiyar mata da kananan yara, tare da ware kayan aiki don muhimman tsare-tsare na yaki da cututtuka, in ji gwamnan.
A nasu jawabin, ministan kiwon lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate da takwaransa karamin ministan ma’aikatar ta kiwon lafiya, Iziaq Adekunle Salako, sun jaddada bukatar hada kai don cimma nasarar samar da yanayin kiwon lafiya na duniya nan da shekarar 2030.
“Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta mayar da hankali ne wajen farfado da fannin kiwon lafiya domin cimma nasarar samar da kiwon lafiya ta duniya nan da shekarar 2030 ta hanyar ba da fifikon bayar da horo da horarwa tare da inganta ababen more rayuwa da kula da lafiyar mata masu juna biyu,” in ji Farfesa Pate.
Shehun Dikwa, Ibrahim Ibn Umar El-Kanemi, wanda ya wakilci mai martaba Shehun Borno ne ya jagoranci sauran sarakuna, da masu rike da sarautar gargajiya a jihar zuwa wajen taron.