Daga, Sani Gazas Chinade Damaturu
Wata gidauniyar bada tallafi mai zaman kanta mai suna Amputee Foundation a Yobe, ta bukaci a tallafa wa yara uku da suka samu raunuka sakamakon tashin bam.
Shugaban kuma wanda ya kafa gidauniyar, Mista Tizhe Kwaji, ne ya yi wannan roko a wani taron bayar da abinci a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Ya ce wadanda harin bam din ya rutsa da su ‘yan shekaru 8, 10, 1 ne, inda ya kara da cewa yanayin da suke ciki “abin ban takaici ne mai raɗaɗi kan mummunan tasirin irin waɗannan abubuwan ga rayuwar matasa manyan gobe”.
Mista Kwaji ya nuna damuwarsa kan yadda lamarin ya shafi rayuwar wadanda lamarin ya shafa, inda ya jaddada bukatar su na neman ilimi da kuma gyara dukannin harkokin rayuwar su.
Ya ce, “Ilimi ba gata ba ce kawai; shi ne mabudin su na samun kyakkyawar makoma, amma ba za mu iya yi mu kadai ba, muna bukatar goyon bayan ku.”
Kwaji ya bayyana kudurin gidauniyar na karfafawa nakasassu ta hanyar dabarun fasaha, samar da abinci da tallafin kudi, da kuma kulawa.
Wanda ya kafa gidauniyar ya yi kira ga gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, da Mohammed Abba Isa, mai baiwa shugaban kasa shawara kan al’amuran nakasassu (PLWD) da su tallafa wa kokarin gidauniyar a Yobe da sauran jihohi.
Ya kuma bukaci jama’a da su bayar da tasu gudummuwa a wannan harka, tare da jaddada muhimmancin bayar da agaji.
Hafsat Muhammad wadda ta ci gajiyar tallafin gidauniyar ta nuna jin dadin ta ga gidauniyar tare da karfafa gwiwar sauran ‘yan Najeriya da su yi koyi da ita.