Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiMai Kaltungo ya Jagoranci koyar ma da Al'ummar shi nomar Rogo a...

Mai Kaltungo ya Jagoranci koyar ma da Al’ummar shi nomar Rogo a zamanance

Daga RABIU SANUSI a Kano

Al-ummar daga Ture Balam cikin masarautan Kaltungo sun amsa gayyatan Uban k’asa Mai Kaltungo don noman ciyawa a gonan Uban Kasa na al-umma dake cikin garin Ture Balam.

wannan zamu iya cewa Kamar yadda aka sani wannan gona ta Rogon Uban Kasa Mai Kaltungo ya noma ne don ya taimaki al-ummar sa.

Haka kuma duk lokacin da wani aiki ya tashi na wannan gonar al-ummar garin Ture Balam su suke gabatar da aikin tun kama daga dashen rogon, noma zuwa girbin rogon kuma gonane da Uban Kasar Kaltungo yayi don ya taimaki Jama’ar dake karkashin ikon masarautar shi.

Wakilin mu yadai Kalato mana cewa wadanda zasufi cin gajiyan wannan gona su ne al-ummar garin Ture Balam cikin masarautan Kaltungo.

Haka zalika Uban Qasa engr Saleh Muhammad ashekaran daya gabata angudanar da irin wannan kokari a garin Ture Okwaldi inda al-umma sun amfana da Rogo bayan ciran Shi.

Sannan kuma sun koyi yadda ake dashen rogo na zamani tareda samu irin da suka dasa Uban k’asa yayi bankwana dasu.

A wannan shekara kuma Uban Kasa ya garzaya zuwa wani gari daga cikin masarautan sa wato Ture Balam wanda idan Allah ya kaimu aka cire wannan rogon suma sun koyi yadda ake dashen rogo na zamani kuma sun samun irin dashe da abinchi.

”Ashekara mai zuwa kuma Uban Kasa zai Kara garzayawa zuwa wani bangare na Masarautan Kaltungo don cigaba da gabatar da wannan aikin alheri.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments