Daga Rabiu Sanusi
An bayyana shirin maido da martabar Karamara Hukumar Rogo dake jihar Kano bisa turbar da ta dace ta asali dan samun canji mai dorewa.
Sabon shugaban karamar hukumar Hon Mustapha Abubakar Rogo ne ya bayyana haka a wata ziyarar aiki da manema Labarai suka kai ofishin sa.
Hon Abubakar Rogo yace duba da irin ta’adin da akayi ma Sakatariyyar karamar hukumar ma wani abin dubawa ne musamman yadda aka sace da kwashe komi.
shugaban karamar hukumar ya bada misalin yadda ita kanta sakatariyya yadda suka sameta wani abin Allah wadai ne.
”Yanzu haka idan kuka duba nan cikin ofishi na babu nazurar sanyaya daki har guda biyu an sace,kaga sauran ofisoshin ma abin sai wanda yagani.”
Abubakar Mustapha ya tabbatar da cewa wannan Karamar hukuma ba cikin wani halin da dole sai an samu hadin kai daga sarakunan gargajiya da saurna dukkan masu ruwa da tsaki dan ceto wannan yanki mai tarihi.
”idan baku manta ba mun yi wannan jagoranci a lokacin baya kuma ba sai mun fadi abubuwan da muka yi ba,Al’umma shaida ne bama cika baki.
”Muna da matasa da Mata da yakamata mu kawo masu tallafin da zai shiga lungu da sako a wannan karamar hukuma ta Rogo dan haka zamuyi duk mai yuwuwa wajen kawo sauyi.
Shugaban ya kara tabbatar da kokarin samo hanyar da za’a cigaba da inganta hanyoyi dake fadin karamar hukumar dan tallafama mazauna Karkara musamman manoma.
”yanzu zamu kara kokartawa wajen cigaba da ganawa da sauran masu ruwa da tsaki dan samo hanyar kawo dauki kan abinda ya shafi tsaro,musamman yadda muke kan iyaka da Katsina da Kaduna.
Alhaji Abubaka Mustpha ya kara da batun inganta harkar lafiya dan samama mata da yara kamar yadda shi kan sa mai Girma gwamna Abba Kabir ke fadi tashin taimakawa jihar baki daya.
”Da wannan muke amfani da wannan dama wajen godiya ga shugaban tafiyar Kwankwasiyya Engr Rabiu Kwankwaso da mai girma Gwamnan Kano tare da shi kansa Shugaban Majalisar Dokokin jihar wajen tabbatar da shugabanci nagari a wannan jiha.
Rogo ya kuma godewa dukkan sauran masu ruwa da tsaki na karamar hukumar ta Rogo wajen irin hadin kan da suke basu a wannan tafiya da suka fara.