Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiIPMAN: Fayyace Gaskiya

IPMAN: Fayyace Gaskiya

Daga Rabiu Sanusi

Matatar mai ta Dangote tana son ta fayyace cewa ba ta karɓi wani kudi daga kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN ba domin siyan kayan da aka tace.

ya tabbar da cewa ana ci gaba da tattaunawa da kungiyar ta IPMAN, amma abin takaici ne a ce su (Mambobin IPMAN) suna fuskantar matsalar lodin kayan da aka tace daga matatar man fetur dinmu, domin a halin yanzu ba mu da wata huldar kasuwanci da su.

Saboda haka, ba za a iya ɗaukar alhakin duk wani kuɗin da aka yi wa wasu ƙungiyoyi ba.

An biya kudin da aka ambata ta hannun Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), ba mu ba. Hakazalika, NNPCL bai yarda ko ba mu izini mu saki Premium Motor Spirit (PMS) ga IPMAN ba.

”Muna so mu jaddada cewa za mu iya biyan bukatun al’umma na duk wani nau’in man fetur da suka hada da man fetur, dizal, da man jiragen sama.

Yace ahalin yanzu, muna iya lodin manyan motoci 2,900 a kowace rana, haka kuma muna kwashe kayayyakin man fetur ta ruwa.

”Muna ba IPMAN shawara da ta yi rajista da mu kuma ta biya kai tsaye saboda muna da isassun albarkatun man fetur don biyan bukatun membobinsu.

Bugu da kari kuma, muna ganin yana da kyau duk masu ruwa da tsaki su guji furta kalamai marasa tushe a kafafen yada labarai, domin hakan na iya kawo cikas ga kokarin sake farfado da tattalin arzikin mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu. Gudanar da kasuwanci ta hanyar hasashe na jama’a ba shi da amfani kuma rashin kishin ƙasa.

Don amfanin ƙasarmu, muna ƙarfafa duk masu ruwa da tsaki su ba da haɗin kai tare da bin shawarwarin Shugaba Tinubu, tare da inganta tsarin haɗin kai, maimakon shiga cikin rikice-rikicen kafofin watsa labaru da farfaganda mara amfani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments