Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Buni Ya Kasafta  Naira Biliyan 320 A Matsayin  Kasafin Kudin 2025

Gwamna Buni Ya Kasafta  Naira Biliyan 320 A Matsayin  Kasafin Kudin 2025

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya gabatar da jimillar kudi N320,811,000,000 a matsayin kiyasin kasafin kudin shekarar 2025 ga majalisar dokokin jihar.

Wannan Kasafin kudi na 2025 mai taken “Kasafin Haɓaka Tattalin Arziki da Rage Talauci an gabatar da shi ga Majalisar dokokin Jihar ranar Alhamis.

Da yake gabatar da kasafin kudin, Gwamna Buni, ya ce an gabatar da kimanin Naira  N144,036,787,000 wanda ke wakiltar kashi 44.9%, a matsayin kasafin kudi na yau da kullum  yayin da aka ware Naira 176,774,213,000 wanda ke wakiltar kashi 55.1% na manyan ayyuka.

Ya kara da cewar, kasafin kudin shekarar 2024, yanayin yadda aka gudanar da shi na nuna samun nasarar kashi 76% zuwa 30 ga watan Satumba 2024.

A cewarsa a shekarar 2025 gwamnatin jihar ta kudiri aniyar gina tituna da gyaran fuska ga wasu domin samar da saukin gudanar da harkokin sufuru ga al’ummar Jihar.

Gwamnati ta himmatu wajen ganin an kammala ayyukan tituna goma sha bakwai da ake gudanarwa, tare da fara wasu sabbin guda goma sha daya, wadda nan ba da dadewa ba za a fara aikin gina gadar sama a  Damaturu fadar Jihar.

Gwamnan ya ce za a kara hakar rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana tare da inganta aikin samar da ruwa da sanya sabbin bututun ruwa a garuruwan Damaturu, Buni-Yadi, Nguru, Geidam da Potiskum.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin sa za ta fara aiki a birnin Damaturu na tattalin arziki, da kuma zage damtse wajen gudanar da aikin gyaran cibiyoyin kula da dabbobi na Nasari, Gurjaje da Bade-Gana tare da sayan kayayyakin gudanar da aikin  gona.

A nasa jawabin ya yin karbar kasafin kudin  kakakin majalisar dokokin jihar Hon Chiroma Buba Mashio, ya ce majalisar za ta yi aiki kan kasafin kudi domin a gaggauta zartar da shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments