Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Hukumar bunkasa Jihohin arewa maso gabas (NEDC) ta kara horar da wasu matasa 45 da aka zakulo daga kananan hukumomi 17 da ke jihar kan mabambanta sana’o’i don ganin sun kara Inganta sana’o’in na su.
Da ya ke mika kayayyakin gudanar da sana’o’in ga wadanda suka amfana, babbban jami’in hukumar ta NEDC a Yobe Dr Ali Abbas ya bayyana cewar, hukumar su ta horar da wadannan matasa ne don su ma su kara habaka sana’o’in su yadda al’umma da dama za su amfana.
Babban jami’n ya kara da cewar mun tanadar wa wadannan matasa ne injunan sarrafa gawayi, aikin na’urori ma su amfani da hasken rana, da makamantan su.
A cewarsa akasarin wadannan matasa maza da mata tun tunin da ma can suna gudanar da sana’o’in da aka sake horar da su ne akai ba wai sababbin dauka bane domin in mun ce sabbin matasa za mu dauka domin horar da su, to akwai yiwuwar in mun horar da su muka ba su injunan gudanar da sana’o’in akwai yiwuwar su sayar da injunan ba tare da sun amfana ba.
Ya Kara da cewar wadannan matasa 45 sun zo ne a matsayin gwaji domin mun kudiri aniyar horar da matasa kimanin 558 ne da za mu zakulo su daga kowace karamar hukumar 17 da ke Jihar ta Yobe.
Dr Abbas ya yabawa Gwamnna Mai Mala dangane da yadda ya ke taimakawa wannan hukuma ta su ta kowane bangare. Kana ya kuma bada tabbacin cigaba da hada gwiwa da gwamnatin Jihar wajen ganin sun gudanar da ayyukan raya kasa ma su yawa a jihar.