Daga Rabiu Sanusi
Mai taimakawa Gwamnan Kano na musamman kan harkokin Waqa da Wallafa Hon Tijjani Hussaini Gandu ya bayyana kudurin mai girma Abba Kabir Yusuf na cigaba da taba rayukan Yan Jam’iyya da kafatanin Al’ummar jihar Kano baki daya.
Alhaji Tijjani gandu ya bayyana hakane a wata zantawa da yayi da manema labarai a ranar Litinin din nan.
mai taimakawa gwamnan yace yazuwa yanzu gwamna Abba Kabir ya yi abubuwan alkhairi da dama wadanda yazuwa yanzu babu makawa Jama’ar Kano sun fahimci inda Gwamna Abba ya dosa.
”Mun sani kamar yadda kuka sani gwamna lokacin yakin neman zabe ya shiga Lungu da sakon jihar Kano tare da yin Alkawari ga Jama’a na ayyukan alkhairi kuma yanzu haka anfara gani a kasa.
Tijjani Gandu ya kuma ce wannan ne ya bashi damar komawa mazabar sa ta Gandun Albasa dan yayi koyi da mai girma Gwamnan Kano bisa abin alkhairi.
”A yanzu haka nafara bada mashina masu amfani da hasken rana,inda na baiwa mutane shidda(6) dan cika alkawarin da nayi na zama Gwamnan su na Gandu.
Ahmad Tijjani Gandu ya kara da cewa ya zuwa yanzu Gwamnan ya tabbatar wa da wasu Yan gwagwarmayar Jam’iyyar NNPP musamman mawaka da mawallafa motocin hawa dan tabbatar da alkwarin da ya Dauka.
Mai bawa gwamnan shawara ya kuma bukaci sauran magoya ba ya dasu kara hakuri kan abinda gwamnan ke kokarin yi na karade kaf sauran da basu samu nasu rabon ba suma suna kan layi.
Gandu Ahmad ya kuma bukaci magoya baya dasu cigaba da yima wannan gwamnati mai albarka addu’a dan asamu nasarori.