Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLafiyaUNICEF Ta Taimakawa Jihar Borno Kan Cutar Kwalara

UNICEF Ta Taimakawa Jihar Borno Kan Cutar Kwalara

Daga Ahmed Liman kingimi

A wani yunkuri na yaki da barkewar cutar kwalara a jihar Borno, asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayar da gudummawar muhimman kayayyakin yaki da cutar kwalara da darajarsu ta kai Naira miliyan 113.

Tallafin wanda ya hada da kayyakin cutar gudawa mai saurin yaduwa (AWD) guda 30, da kayayyakin yaki da cutar kwalara guda 90, da gadaje 50 na kwalara, mataimakin wakilin UNICEF a Najeriya, Dr. Rownak Khan ya mika wa ma’aikatar lafiya ta jihar Borno.

Kwamishinan lafiya da ayyukan jin kai ne ya ayyana barkewar cutar a ranar 4 ga Oktoba, 2024, inda sama da 450 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara a jihar. Yankunan da lamarin ya fi shafa sun hada da Maiduguri Metropolitan Council (MMC), Jere, Konduga, Mafa, da Monguno. Abin farin ciki, har yanzu ba a sami rahoton mace-mace ba.

Yunkurin mayar da martanin UNICEF a jihar Borno ya ƙunshi ayyuka da dama kamar inganta tsafta, samar da ruwa, alluran rigakafi, da matakan tsafta. Sama da mutane 13,750 a sansanonin ‘yan gudun hijira daban-daban sun ci gajiyar girka matsugunan gaggawa, tare da raba wasu kayan tsafta da kwalara ga gidaje.

Bugu da kari, UNICEF ta samar da tsaftataccen ruwan sha ga mutane 43,689 a fadin sansanonin ‘yan gudun hijira da dama ta hanyar daukar ruwa na gaggawa da kuma gyara rijiyoyin burtsatse. Kungiyar ta kuma samar da allurar rigakafin cutar kwalara 300,000 ga jihar Borno, inda mutane 290,000 a yankunan da ake fama da cutar tuni aka yi musu rigakafin.

Don ci gaba da inganta sa ido da gano al’amura, UNICEF ta tura ma’aikatan kiwon lafiya 54 da ma’aikatan tallafi a sansanonin. Kungiyar ta ci gaba da taka rawar gani wajen daidaitawa da aiwatar da shirin daukar matakan dakile cutar kwalara tare da hadin gwiwar cibiyar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments