…..Yayin da hanyoyin da suka sada Karamar hukar da Kauyuka suka zama abin azo Agani
Daga Rabiu Sanusi
Yankin Karamar Hukumar Rogo Karamar Hukuma ce a jihar Kano da halin yanzu baza’a iya mantawa da ita musamman yadda take da wani jigo a cikin Gwamnatin dake ci a yanzu.
wannan jigo baya wuce namba 3 a matakin jan ragamar wannan jiha da take da tarihi ta fuskoki daban-dabana fadin Afirika bawai a kasar najeriya kadai ba.
haka zalika bayan shi wannan namba ukku da ake kallon karan shi yakai tsaiko ta fuskar zartar da dukkan wata doka ko abinda yake kama da haka a fadin jihar akwai akwai wasu dayawan gaske da summa suke fada aji awannan jiha.
amma abin takaici idan ka dauki irin rawar da suke takawa na fada aji a cikin jihar ko a gwamnatance basu magance matsalar hanyar da suke da ita ba,wanda idan kata da hanyar makarfi zuwa cikin karamar hukumar ta Rogo babu wata hanya da zata sada ka da sauran mazabu ko kauyukan dake wannan yanki cikin dadin Rai.
wani abin takaici ma baya wuce yadda hanyar data tashi daga cikin karamar hukumar ta Rogo zuwa mahaifar shi kansa namba 3 da tafi kowace hanya a yankin lalacewa tsawo shekaru goma sha wani abu da ake faman yin alkawura yayin yakin neman zaben da yan siyasar yankin suke yi da ita suke yi.
bayan shi namba 3 a jihar akwai dan majalisar Tarayya da jiha haka zalika sanata masu wakiltar wannan yanki amma suk kasa maganace wannan matsalar ta hanyoyin da baza’a ta wuce shurin masaki ba.
yayin da wakilin mu yake zagayawa wannan yanki yayin gudanar da aikin shi yayi Tozali da wasu Al’umma da dama da suke rayuwa a wannan yanki da mafi yawa sukayi Allah wadai da shugabancin wakilan da suke turawa su wakilce su da basuyi masu abinda suka yi alkawarin zasuyi yayin yakin neman zabe.
”Wani abin birgewa a wannan yanki shine yadda al’umma suna kokari wajen neman hanyar dogaro dakai ta fuskar Noma da kiwo da jaraba Kasuwanci.”
Amma dai duk da kokarin da jama’ar suke yi na ganin sun dogara da kansu babu wani abin azo a gani na tallafin kasuwanci ko makamancin hakan da suke samu daga Yan siyasa daban daban.
Haka zalika karin abin bakin cikin ma bai tsaya kan rashin hanyar wucewa ba kadai harda ma batun samar wa matasa aikin yi da a yanzu Rogo take da yawan Matasa da suka kammala karatu ba tare da aikin yi ba.
A bangaren Tsaro kuwa wani abin takaici shine yadda manoma ko Yan Kasuwa idan zasu zo Kasuwa ko dakko kayan Gonar da suka noma yazuwa gidajen su ko Gonakin su yayin da suka zo wajen jami’an tsaro suna bada wani kudin da yazama kamar haraji ne jami’an tsaron suka sanya masu kafin suwuce.
”amma kuma mafi akasarin abinda ke faruwa na karbar na Goro da Jami’an tsaro keyi nada nasaba da rashin kulawar da basa samu daga manyan su na alawus-alawus da ake basu dayawan su basu samu kamar yadda bincike ya nuna.”
”Tabbas dukkan wanda yasan karamar hukumar ta Rogo yasan tana iyaka da jihohin Katsina da Kaduna da suke fama da rashin tsaro ta fukoki da daman gaske.
Da yawan mazauna yankunan suna kokawa da rashin cikakken tsaro dake kara basu ciwon kai tare da Fargaba da barazanar komi zai iya faruwa a lokaacin da ba’a zace shiba.
a wani bincike da wakilin mu ga gabatar yayin ziyarar aiki da yakai a wannan yanki na Rogo ya gano cewa babban abin da ke cima wannan yanki na Falgore shine yadda garin yake fama da rashin wutar lantar ki kusa tsawon shekaru 20 baya da suka gabata babu wutar lantarki a garin na namba 3 da mai karatu yaji ba lallai ya yarda da wannan bayaniba.
A jawabin da yawan mazauna kauyukan da suke kanhayar da ta taso daga Rogo zuwa Falgore da suka hadar da Rinji,Gidan Jatau ko Chidari,Gidan Baso,Kadana’Zarewa,Zare har zuwa Bari sun bayyana takaicin su na zaben shugabanin da sukeyi a shekarun baya zuwa yanzu.
Haka zalika sunce akwai Gadojin da tsawon lokaci babu hanya mai inganci tare da basu damar tafiya da kayansu na Kasuwa da Ayuka yau da Kullum da suke aiwatarwa a kan wannan Hanya.
”akwai hanyar da tashiga zuwa wani kauye da ake kira Gwangwan a nan Karamar Hukumar tamu ta Rogo Wallahi kafin kaje wannan gari sai ranka yayi matukar bacci dan alamun kyau na hanya babu ko Kadan babu kamar ya yanzu lokacin Damina.
”babu abinda yafi yimana ciwo sama da yadda muke da Speaker matakin na ukku a jihar Kano kuma bashi da wata hanya da zaije mahaifar sa sama da wannan hanya amma kusan shekara biyu da hawansa mulki ba zo ya gyara hanyar nan ba,kaga dole muce bamu da Jagorori.
Mazauna yankin sun kuma kara bayyana cewa mutane sun Gaji d irin alkawuran da dayawan Yan siyasa suke masu yayin yakin neman zaben da suke zuwa da bazaka kara ganin Qeyar wani daga cikin su ba har sai lokacin wani zaben Yazo.
”Muna da Yakin Gwamna Abba Kabir Yusuf na yanzu mutumin Kirki ne amma wasu basu cancanta ba sun zagaye shi,sun hana shi yayi aikin daya kamata,dukkan wanda suka hau wata kujera daga wannan yanki namu sai da sukazo yawan yakin neman zabe da yawan su akan Mashina ake biyo dasu zuwa wadannan yankuna namu.
”Bawan Allah abinda yafi mana ciwo shine yanzu akayi mana Mutuwa a wannan lokaci na damina to ina tabbar maka ida ana ruwa sai dai ya dauke koda zai kai kwan biyu ko Ukku sannan muje wajen rufe Gawar Mamacin.”
Wakilin namu ya kalato cewa akwai hanyar data hada wannan Gari na Falgore da Karamar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina da dayawan gaske sai dai mazauna yankin su zagaya idan yazama dole zasuyi wani abu ko batun daukar marassa lafiya ko Matsalar Rashin Lafiya duk da babu cikakken tsaro.
haka zalika yankin dai na kuma fama da karin matsalar samun kyakkyawar kulawa wajen abinda ya shafi Ilimi da shine kashin bayan dukkan wata Al’umma tagari da har yanzu suna bukatar Kulawa dukka cewa gwamnan kano na yanzu yana bakin kokarin shi wajen farfado da shi.
Wakilin mu ya ruwaito cewa wannan yanki yana bukatar hada hannun dukkan wakilcin shugabancin da suka tura da suka hada da shi Kansa Speaker na jiha,Sanatan Kanota Kudu, Dan Majalisar Tarayya dana jiha da sauran masu fada aji a wannan yanki tare da mai Girma Gwamna da suke da tabbacin zai yi su shigo su tallafawa wannan karamar hukuma ra Fuskar Hanyoyi,Wutar Lantarki,Inganta Ilimi da saura ababen more rayuwa.