Saturday, April 26, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiBullar Kwalara; Gwamnatin Yobe Ta Mika Magungunan Rigakafi Ga Al'ummomin Da Abin...

Bullar Kwalara; Gwamnatin Yobe Ta Mika Magungunan Rigakafi Ga Al’ummomin Da Abin Ya Shafa

Daga, Sani Gazas Chinade Damaturu

Biyo bayan mutuwar mutane hudu a al’ummar Jangalawaji da Tadangara dake karamar hukumar Gujba sakamakon bullar wata  cuta dake haifar da gudawa, gwamnatin jihar Yobe ta fara gudanar allurar rigakafi da kuma gangamin wayar da kan jama’a cikin  al’ummomin da abin ya fi shafa da kewayen su domin dakile yaduwar cutar.

Sakataren zartarwa na hukumar kula da lafiya a matakin farko na jiha, Dr.Babagana Kundi Machina wanda ya samu wakilcin jami’in kula da harkokin kiwon lafiya na jiha, Mohammad Gado ya bayyana manufarsu akan ita ce kara wayar da kan jama’a game da rigakafi da magance cutar a matakin farko.

“An samu bullar cutar gudawa a wannan yanki wanda ya yi sanadin asarar rayuka, don haka mun zo ne domin kara wayar da kan jama’a kan musabbabin cutar da kuma rigakafin.”

“Hakan ya faru ne sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a baya-bayan nan inda wadannan al’ummomin da ke kewaye da ruwa suka kamu da cutar.

Tsarin tsafta yana da matukar muhimmanci musamman a wannan lokacin da cutar ta bulla,” in ji shi.

Hakimin yankin Lamido Modu wanda ya yi maraba da tawagar, ya godewa gwamnatin jihar Yobe kan matakan da ta dauka na tabbatar da kare rayukan al’umma daga kamuwa da cutar.

“A matsayinmu na shugabannin al’umma, muna gode muku don samun lokaci don ziyartar mu da kuma ba mu ƙarin sani game da wannan cuta wadda zuwanku ya nuna irin sadaukarwar da gwamnati ta yi wajen samar da ayyukan jin dadin jama’a”

“Akwai tawagogin likitoci uku da suka ziyarce mu tun bayan barkewar wannan cuta kuma mun yi godiya matuka” inji shi.

Hakimin ya kuma roki gwamnati da ta tona rijiyar burtsatse ga al’umma domin sama da mutane 3,000 sun dogara da ruwan rijiyoyi da rijiyoyin burtsatse don amfanin mutane da dabbobi.

Tawagar ta mika allunan Aqua, Magungunan tsayar da gudawa (Rehydration) , na’urorin tsafta da sauransu ga Hakimin Gundumar don ci gaba da rabawa ga al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments