Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiAl'ummar Kudancin Borno Sun Jajantawa Zulum, Sun Ba Da Gudummawar Naira Miliyan...

Al’ummar Kudancin Borno Sun Jajantawa Zulum, Sun Ba Da Gudummawar Naira Miliyan 200

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Mataimakin Gwamnan Jihar Borno Dr Umar Kadafur ya jagoranci masu ruwa da tsaki daga yankin Kudancin Borno domin jajantawa Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum da wadanda suka mutu a makon jiya sakamakon bala’in ambaliyar ruwa a Maiduguri da karamar hukumar Jere ta shafa yadda fiye da mutane miliyan biyu suka rasa muhallin su.

Hon Kadafur ya samu rakiyar Sen. Muhammad Ali Ndume , Sanata mai wakiltar Kudancin Borno, Hon Bello Ayuba Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Borno, Tsoffin Mataimakan Gwamnoni, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC ta Kudu, Tsohon Ambasada, masu martaba Sarakunan Biu, Shani, Gwoza, Uba, ‘Yan Jihar Borno. Wakilan Majalisar wakilai daga kudancin Borno , Sakatarorin dindindin, tsoffin shugabannin kananan hukumomi na yanzu da na baya, masu ba da shawara na musamman, manyan mataimaka na musamman, shugabannin hukumomi da  tsohon shugaban NLC na kasa Ayuba wabba, masu ruwa da tsaki na APC da dai sauransu.

Sanata Ali Ndume ne ya gabatar da jawabi na farko, inda ya ce bisa umarnin mataimakin gwamna, mun kafa  asusu domin bayar da gudunmuwar hadin gwiwa don tallafa wa ’yan’uwanmu da bala’in ambaliyar ruwa ta shafa.

Ndume ya kara da cewa an tara jimillar miliyan dari biyu kuma har yanzu asusun yana bude domin ci gaba da bayar da gudunmawa.

Mataimakin Gwamnan a lokacin da yake mikawa Gwamnan Cakin miliyan dari biyu (200,000,000) ya jajanta wa wadanda lamarin ya rutsa da su tare da yin addu’ar Allah ya ba su zuciyar jure wannan bala’in da ambaliyar ruwan ta haifar musu, sannan kuma ya tabbatar wa gwamnan cewa har yanzu asusun su yana nan a bude kuma yana karbar gudummawar, a matsayinsa na jagoran Kudancin Borno, yadda ya ba da tabbacin cewa za a gabatar da duk wata gudunmuwar da aka bayar a cikin asusun.

Da ya ke jawabi Farfesa Babagana Umara Zulum bayan ya karbi takardar, ya yaba da goyon baya da jajircewar al’ummar Kudancin Borno, ya kara da cewa wannan shaida ce ta hadin kai a jihar Borno.

“Gwamna Zulum ya jaddada cewa hadin kai ne ya fitar da mu daga matsalolin ‘yan tada kayar bayan da aikin sake gina Borno ya samu nasarori wajen sake ginawa da kuma sake tsugunar da mutanen da ke hijira tare da samun ci gaba mai dorewa a mafi yawan al’ummomin da aka dawo da su.”

Farfesa Zulum ya yi kira ga tawagar da su yi taka-tsan-tsan, kar su bari duk wani dan siyasa ya raba kan jama’a don amfanin kansu, ya kuma bukaci Borno ta tashi tsaye domin samar da zaman lafiya da ci gaba, tare da ba su tabbacin za a yi amfani da gudunmawar da suka bayar ta hanyar da ta dace da yardar Allah.

A fadar Shehun Borno Mataimakin Gwamnan a lokacin da yake mika cak na Naira miliyan goma (10,000,000) ga Mai Martaba Shehun Borno Shehu Abubakar Ibn Garbai El-kanemi a fadarsa, ya jajantawa uban kasar bisa ambaliyar ruwa da fadar ta rutsa da su a lokacin da ruwa ya rutsa da fadar.

Mai martaba Shehun Borno ya mika godiyarsa ga tawagar da mataimakin gwamnan jihar Borno ya jagoranta tare da rakiyar sarakunan kudancin Borno bisa gudunmawar da suke baiwa jihar tare da bukatar  su da su dage da addu’a, hadin kai da ci gaban jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments