Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaAn Roki 'Yan Siyasar Jihar Yobe Da Su Daina Barazanar Kiranye Ga...

An Roki ‘Yan Siyasar Jihar Yobe Da Su Daina Barazanar Kiranye Ga Wasu Wakilan Su

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Ganin yadda ake samun takaddama tsakanin zababbu da ‘yan siyasa a Jihar Yobe, an shawarci jama’a su rika yin hakuri da juna ta bin hanyoyin daukar matakan da suka dace domin fadakar da ‘yan siyasa zababbu game da kura-kuran da ake ganin suna aikatawa lokacin da aka zabe su don yin wakilci.

Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Komred Goni Kolo Shugaban Kungiyar G7 da rundunar adalci reshen arewa maso gabas  a tattaunawar sa da manema labarai dangane da yunkurin da wasu kungiyar ‘yan siyasa ke yi kan cewar za su yi kiranye ga wakilin su Honarabul Lawan Shettima Ali mai wakiltar kananan hukumomin Yunusari, Geidam da kuma Bursari a majalisar wakilai ta kasa a kwanakin baya.

Kwamared Goni Kolo, ya ja hankalin shugabanni su dubi lamarin da ake ciki a rika tallafawa talakawa da ‘yan siyasa ta hanyar kai ziyara yankunan da aka fito tare da sauraron damuwar mutane don a tallafa musu.

Ya ce a matsayin sa na shugaban kungiyar rundunar adalci a shiyyar arewa maso gabas kuma kakakin kungiyar G17 ta hadaka a Jam’iyyar APC na Jihar Yobe, ya bayyana cewa, sune tun fill-azal suka shiga birni da kauye suka yi kamfen don zabar ‘yan siyasa na majalisun Jiha , na wakilai, Sanatoci da gwamnoni aka samar da gwamnati wacce take zababbiya a matakin Jihohi da tarayya.

Don haka ya kamata magoya bayan jamiyyar  APC a jihohin Borno da Yobe su hada Kai a daina cin zarafin zababbun ta hanyar baza jita-jita da labarun karya ko cin zarafi game da su.

Idan sun yi kuskure a jawo hankalin su a nusar da su yadda za su gyara tafiyar su, aci gaba da cin moriyar wakilcin su.

Idan kuma sun bijire a bi ta hanyar shugabannin jamiyyar don a ja musu kunne su gyara kafin a kai ga barazanar yi musu kiranye wannan shi ne mafi zama dai-dai.

Don haka ne kungiyar su ta G17 ta bukaci kowa ya tsarkake ayyukan sa na siyasa don a gina Jihohin da kasa baki daya.

Yace a matsayin su na ‘yan siyasa da suka shiga birni da kauye suka wayar da kai aka zabi shugabanni baza su bari a ci zarafin su ba, amma za su bari a dauki matakin sanar da su inda suka kauce hanya don su gyara.

Saboda idan aka ci zarafin shugabanni da aka zaba za su iya kaucewa su bar mutanen da suke wakilta kuma za a iya rasa alhairan da ake samu ta dalilin su.

Kwamared Goni Kolo ya kara da cewa ba daidai bane yadda ake amfani da kafafen sadarwa na zamani ake cin zarafin dan majalisar wakilai Hon. Lawan Shetima Ali mai wakiltar Mazabar Bursali, Yunusari da Gaidam duk da cewa mutane ne suka tsaya suka fito suka zabe shi.

To amma an wayi gari duk da kokarin da ya ke yi na samar da wakilci na gari a yankin sa, ko yaushe wasu marasa kishi suna damun sa da barazanar yi masa kiranye.

Goni Kolo ya kara da cewa ba komai ke haifar da irin wannan ba ga Hon  Lawan Shetima Ali sai hassada, kuma daga karshe tana cin masu yin hassadar ta yadda idan an dame shi da cin mutunci zai iya kauracewa yankin, abin da ake samu daga hannun sa ko ofishin sa a daina samu, kuma talaka da yayi zabe shi ke da asara.

Don haka ya roki ‘yan siyasa da talakawa da zababbu kowa ya san hakkin da ke kansa a zauna lafiya a ci gaba da adduah Allah ya kawo zaman lafiya a wannan yanki a samu magance matsalar ta’addanci, talauci, yunwa da ambaliyar ruwa da suka addabi jihohin Borno da Yobe da ma sassa da dama na Jihohin arewa maso gabas.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments